Tsohon shugaban kamfanin Nissan ya yi hijira

Asalin hoton, Reuters
Tsohon shugaban kera motoci na Nissan Carlos Ghosn, ya yi hijira zuwa Lebanon bayan ya tsere daga Japan.
Mista Ghosn dai yana fuskantar shari'a kan zargin almundahana a Japan din.
A wata sanarwa da Mista Ghosn din ya fitar, ya bayyana cewa ba wai ya yi hijira bane daga Japan sakamakon yana tsoron hukunci ko kuma shari'a, ya yi hakan ne saboda ya guji ''rashin adalci da kuma muzgunawa irin ta siyasa.''
Lauyansa ya bayyana cewa ya yi ''mamaki'' kan batun hijirar, kuma ya kwana biyu bai yi magana da Mista Ghosn ba.
Har yanzu babu wani cikakken bayani dangane da yadda tsohon shugaban kamfanin ya bar kasar, sakamakon tuni aka hana shi fita daga kasar.
An yi kiyasin cewa Mista Ghosn yana da kadarori na kimanin dalar Amurka miliyan 120, wanda kuma yana daya daga cikin kusoshi a kasuwar motoci ta duniya, kafin kama shi da aka yi a 2018.
Sai dai Mista Ghosn din ya musanta duka zarge-zargen da ake yi masa.
Lamarin Mista Ghosn ya ja hankalin duniya, kuma tsare shi da aka yi ya ja ake sa ido ga bangaren shari'a na kasar Japan.
Mista Ghosn mai shekaru 65, an haife shi a Brazil kuma iyayensa 'yan asalin kasar Lebanon ne, ya kuma yi rayuwarsa ta kuruciya a Beirut.
Daga baya sai ya tafi kasar Faransa inda ya ci gaba da karatu. Mista Ghosin yana da fasfo din kasashen Brazil da Faransa da Lebanon.











