Mahara sun kashe mutun 22 a DR Congo

Felix Tshisekedi yana jagoran babbar jam'iyyar adawa ta DR Congo da mahaifinsa ya kafa

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Felix Tshisekedi yana jagoran babbar jam'iyyar adawa ta DR Congo da mahaifinsa ya kafa
An wallafa

Hukumomi a gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo sun ce akalla mutum 22 ne suka mutu a wani hari da 'yan tayar da kar baya na ADF daga Uganda suka kai a garin Beni da ke yankin Nord Kivu.

Maharan sun yi amfani da adduna da bindigogi wajen kashe fararen hula, a cewar shugaban kungiyoyin farar hula a garin Mayimoya inda lamarin ya faru.

Kungiyoyin na cewa mamatan sun hada da namiji 15 da kuma mace biyar. Ko a ranar Juma'a , sai da wasu da ake zargin mayakan ADF ne suka kashe mutum shida a Beni.

A watan Agusta ne shugaba Felix Tshisekedi ya yi nemi a kafa rundunar hadin gwiwa a yankin domin yakar 'yan ta'adda a gabashin kasarsa.

Rundunar sojin ta yi nasarar kashe 'yan tayar da kayan baya da kwamandojinsu da dama, yayin da wasu daruruwa suka mika wuya.

Sai dai kuma hakan ta haifar da karuwar hare-hare da kuma yin barazana ga fararen hula a yankin gabashin kasar.

Karuwar hare-haren 'yan tayar da kayar baya na ADF ta haifar da kazamar zanga-zanga da fararen hula da zargin dakarun Majalisar Dinkin Duniya da gazawa wajen ba su kariya.