DR Congo: Wajen hakar ma'adinai ya rufto ya kashe mutane

Asalin hoton, AFP
A kalla mutum 36 ne suka mutu bayan da wajen hakar ma'adanan kofa ya rufto a lardin Lualaba da ke kudu maso gabashin Jamhuriyar Dimokradiyya Congo, a cewar hukumomi.
Gwamnan lardin Richard Muyej ya zargi masu hakar ma'adinai babisa ka'ida ba da jawo faruwar lamarin.
Hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba a yankin ya zamar wa mutane abin yi don samun kudi.
Hakar ma'adinai a Jamhuriyar Dimokradiyya Congo na samar da fiye da rabin ma'adinin cobalt na duniya - wanda ake amfani da shi wajen hada batirin waya.
Farashinsa ya ninka sau biyu a bara saboda bukatarsa da ake da ita wajen hada motoci masu aiki da wutar lantarki, wanda nan ma ake amfani da ma'adanin wajen hada batiransu.
Lamarin ya auku ne a ranar Alhamis a kamfanin ma'adani na Kamoto, wani bangare na na babban kamfanin hakar ma'adanai na Swiss Glencore, wanda yake kusa da birnin Kolwezi na Lualaba.
Akwai yiwuwar a samu karin gawarwaki a yayin da masu aikin ceto ke ci gaba da zakulo mutane a wajen, kamar yadda wakilin BBC Gaius Koweneya ruwaito daga Kinshasa.
A wata sanarwa da ya fitar, kamfanin Glencore ya ce mutum 19 ne suka mutu amma ya kara da cewa akwai yiwuwar mutuwar wadansu da ba a tabbar ba.
Ya kara da cewa masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba na yawan zuwa wuraren hakar kamfanin a boye.
"Hakan ya jawo turuwar masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba kamar 2,000 a kowace rana.
Hakan na jawo matukar barazana ga ma'aikatanmu da kayan aikinmu da su kansu masu hakar ma'adanan ba bisa ka'ida ba."
Gwamnan lardin Lualaba Richard Muyej ya kuma zargi masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba da jawo hatsarin:
Jamhuriyar Dimokradiyya Congo dai ta kasa amfani da albarkatun kasar da take da shi wajen azurta miliyoyin al'ummarta da ke fama da talauci.











