Majalisar Kano ta amince da dokar sabbin masarautu

Asalin hoton, Getty Images
Majalisar dokokin jihar Kano ta sa hannu kan dokar nan mai cike da ce-ce-ku-ce ta kirkiro sabbin masarautu a jihar, wadda ta bukaci a kirkiro karin masarautu hudu a jihar.
An sa hannu kan dokar ne a yau Alhamis bayan da majalisar zartarwar jihar ta aikawa majalisar dokokin da ita ranar Litinin.
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan wata kotu a Kano ta soke sabbin masarautun da aka kafa a baya, inda ta ce ta yanke wannan hukunci ne saboda an shigar da kudurin bukatar kirkirar masarautun ba bisa ka'ida ba.
A wata sanarwa da kwamishinan watsa labarai na jihar Kano Malam Muhammad Garba ya fitar, ya bayyana cewa majalisar zartarwa ta jihar ta sake aika wani sabon kudiri da zai bayar da damar kafa masarautar Rano da Gaya da Bichi da kuma Karaye.
Kwamishinan ya bayyana cewa an gyara kudirin dokar masarautu ta 2019 ne saboda gyaran ya shafi jama'a.
An yi gyara a Bangare na 12, wanda 'yan majalisar suka kara wani sharadi na cewa sai gwamna ya nemi amincewarsu kafin ya daga darajar sarakunan zuwa daraja ta daya da ta biyu da ta uku.
A ranar 21 ga Satumban 2019 ne Mai Shari'a Usman Na'abba na babbar kotun jihar Kano ya soke dokar farko da majalisar ta yi na kirkiro masarautun Karaye da Gaya da Bichi da Rano, inda ya ce ba a bi ka'ida ba yayin yin ta.
Daga nan ne kuma 'yan majalisar suka daura aniyar sake yin dokar ta hanyar da ta dace bisa kudirin da gwamnati ta aike masu. A baya dai cikin kwana daya aka kai kudiri kuma aka kaddamar da dokar.









