NLC: Gwamnatin Najeriya da kungiyoyin kwadago sun cimma matsaya

Festus Keyamo, Chris Ngige, Ayuba Wabba

Asalin hoton, @fkeyamo/Twitter

Bayanan hoto, Kafin a cimma matsayar, kungiyar kwadagon ta bukaci a yi wa ma'aikatan da ke karbar albashin da ya haura naira 30,000 karin kashi 29 cikin 100
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Shugabannin Kungiyar Kwadago ta Najeriya da wakilan gwamnatin kasar sun cimma matsaya kan mafi karancin albashi na naira 30,000 da safiyar Juma'a, kamar yadda karamin ministan kwadago Festus Keyamo ya bayyana.

Bayan tattaunawar da aka kwashe kusan kwana uku ana yi, shugabannin kungiyar da wakilan gwamnati sun gaza amincewa kan lamari guda da ya shafi tsare-tsaren albashi 12 na ma'aikatan gwamnati.

Yarjejeniyar ta amince cewa ma'aikata da ke mataki na 7 zuwa na 17 za su samu karin albashi na tsakanin kashi 14 zuwa kashi 23 cikin 100, yayin da wadanda ake biya albashi na musamman da ake kira CONHESS za su samu karin albashi na kashi 23.3 zuwa kashi 10.5 cikin 100 a mataki guda.

Kafin a cimma matsayar, kungiyar kwadagon ta bukaci a yi wa ma'aikatan da ke karbar albashin da ya haura naira 30,000 karin kashi 29 cikin dari da wadanda suke mataki 11 ziwa 17.

Mafi karancin albashi na Naira 30,000 ya zama doka a Najeriya tun a watan Afrilun 2019 amma yadda manyan ma'aikatan gwamnati za su amfana da sabon tsarin ya sa gwamnati da kungiyar kwadagon tattaunawa tun ranar Talata don gujewa fadawa yajin aiki.

Gwamnatin Najeriya ta fara tattaunawa da Kungiyoyin Kwadagon na NLC da TUC ne bayan da suka yi barazanar fara yajin aiki ranar 16 ga Oktobar 2019.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

lABOUR Leaders

Kafin fara tattaunawar, bangarorin biyu sun ce suna fatan cimma matsaya mai dorewa.

Shugaban kungiyar NLC, Ayuba Wabba ya ce burinsu shi ne su kammala tattaunawa, amma zai ya bayyana masu halin da ma'aikatan gwamnati ke ciki.