NLC ta gaza fara yajin aikin ma'aikata a Najeriya

Shugabannin kungiyar kwadago da kuma wakilan gwamnati a Najeriya za su ci gaba da tattaunawa a ranar Laraba da misalin karfe biyu na rana don cimma yarjejeniya kan batun ko gwamnati za ta biya N30,000 mafi karancin albashi ga ma'aikata.
Babban kalubalen shi ne yadda kungiyar kwadago ke bukatar a kara kashi 29 cikin 100 ga ma'aikatan da ke karbar albashin da ya haura N30,000 da kuma wadanda suke matakin aikin gwamnati na 11 zuwa 17.
Kungiyar kwadago da kuma ta 'yan kasuwa sun bai wa gwamnatin Najeriya wa'adin sati biyu na ta fara aiwatar da biyan mafi karancin albashin 30,000 ko kuma su tsunduma yajin aiki a ranar 16 ga watan Oktoba 2019.
To sai dai zai yi wuya a shiga yajin aikin la'akari da cewa ana ci gaba da tattaunawa a tsakanin bangaroran biyu a yau Laraba.
A watan Afrilu ne gwamnati ta aminta da biyan mafi karancin albashi wanda hakan yasa ma'aikata su ka yi maraba da labarin.
To sai dai ga mafi yawa murna ta koma ciki,bayan da gwamnatin ta sanar da cewa kananan ma'aikata kawai karin zai shafa.
Hakan ya harzuka kungiyar kwadago, inda ta dauki matakin tsunduma yajin aiki a ranar 16 ga watan Oktoba.
Kafin zaman na yau, ministan Kwadago Chris Ngige ya jaddada cewa idan har gwamnati ta aminta da muradin kungiyoyin to kuwa tattalin arzikin ta zai shiga cikin matsala kamar na Venezuela.
Mr Ngige ya kara da cewa kudin da ake bukata gwamnati ta kashe wurin biyan ma'aikata zai hana ta gudanar da ayyuka kamar gina hanyoyi a asibitoci da makamantan su.
Ko a ganawarsa da shugabannin kungiyar kananan hukumomi, Mr Ngige ya ce ya yi matukar mamakin jin cewa kungiyar kwadago na shirin shiga yajin aiki kan karin albashi ba tare da sun tattauna bukatunsu da gwamnatocin jihohi ba.
Ya kara da cewa yin barazanar yajin aiki ba tare da bin ka'idoji ba sabawa dokar kwadago ta duniya ne.
Ministan ya zargi kungiyar da yiwa ma'aikata rufa rufa kan yadda al'amarin karin albashin yake, inda yace yanzu haka gwamnati na kan bitar yadda tsarin biyan albashi daban daban yake a halin yanzu.
To sai dai wata kungiyar ma'aikata ta United Labour Congress ta ce ba za ta shiga yajin aikin ba kasancewar kungiyoyin ba sa magana da murya daya.
Mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta kasa Comrade Amaechi Asugwuni ya ce a yau Laraba ne za su yanke hukunci ko za su tsunduma yajin aikin ko akasin haka.











