Ngige bai dace da ma'aikatar kwadago ba – NLC

Bayanan sautiHirar Khalifa Shehu Dokaji da shugaban kungiyar Kwadago ta NLC Ayuba Wabba
An wallafa

Latsa alamar lasifika a hoton sama domin sauraren hirar da BBC ta yi da Kwamred Ayuba Wabba

Kungiyar kwadago a Najeriya ta nuna rashin jin dadinta kan sake bai wa Chris Ngige ministan ma'aikatar kwadago karo na biyu.

Shugaban kungiyar kwadago a Najeriya kwamared Ayuba Wabba wanda ya yi korafin, ya shaidawa BBC cewa, "Ngige bai cancanta ya jagoranci ma'aikatar ba idan har gwamnati tana son yin aiki mai kyau da ma'aikata.

Tun bayan kawo karshen wa'adin mulkinsa na farko, Shugaba Buhari ya yi ikirarin cewa ministocinsa sun taka rawar gani, kuma shi ne dalilin da ya sa ya ci gaba da tafiya da wasu daga cikinsu.

A ranar Labara ne shugaba Buhari ya sake rantsar da sabbin ministocinsa 43, kuma cikinsu akwai 12 da ya fara aiki da su a wa'adi na farko kuma cikinsu har da Chris Ngige.

Bayan sake rantsar da shi a matsayin ministan kwadago, Dakta Chris Ngige, ya yi alkawarin gaggauta aiwatar da sabon shirin mafi karancin albashi.

An dai kai ruwa rana tsakanin ministan da kuma kungiyar kwadago kan batun karin albashin na ma'aikata, kafin shugaba Buhari ya amince da karin albashi mafi karanci na naira 30,000 a watan Afrilu.

Shugaban ya amince da matakin ne bayan kungiyar kwadago ta NLC ta bai wa shugaban wa'adi ya amince da dokar ko ta tsunduma yajin aiki wanda zai shafi kowane ma'aikaci.

A wa'adin mulki na farko, kungiyar malaman jami'o'in gwamnati a kasar ta shafe watanni tana yajin aiki kan wasu bukatun da suka shafi inganta ilimin jami'o'in da kuma albashinsu.

Wabba ya ce sun zata za a kawo wanda ya fahimci matsalolin ma'aikata, da sanin doka, idan har ana son a ci gaba da samun zaman lafiya da fahimta.

"Ba a sake dawo da wanda yake kamar soja ba, wanda kullum sai an yi ta daga da shi," in ji shi.

Ya kuma ce idan har gwamnati ta sake jan kafa kan wasu bukatunsu, za su ci gaba da daukar matakin da suka saba dauka.

Kungiyar Kwadago ta NLC ta taba kaddamar da zanga-zanga ta yin kiran a tsige Chris Ngige daga ministan kwadago.