Gas din girki ya fashe ya kashe mutum 10 a Indiya

Collapsed building due to a cooking gas cylinder blast

Asalin hoton, ANI

Bayanan hoto, The two-storey building collapsed due to the blast
An wallafa

A kalla mutane 10 ne suka mutu bayan da wani gas din girki ya fashe a wani gida a jihar Uttar Pradesh da ke arewacin Indiya, a cewar hukumomi.

Ginin ya fadi ne dalilin fashewar, wanda ya auku a wani gini mai hawa biyu a unguwar Mau ranar Litinin.

Ana ci gaba da ayyukan agaji, yayin da jami'ai ke fargabar cewa akwai mutane da yawa da suka makale a cikin baraguzan ginin.

Makwabta sun shaida wa kafafen yada labaran yankin cewa sun ji wata kara mai karfi, kuma nan da nan ginin ya kama da wuta.

Yogi Adityanath, babban minista a Uttar Pradesh ya bayar da umarnin a yi bincike kan lamarin.

"Babban minista Yogi Adityanath ya duba wannan lamarin da ya faru a wani gida a Walidpur a Mau," babban sakatare Awanish Awasthi ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na PTI.

"Ya mika sakon gaisuwarsa ga iyalan wadanda suka mutu ya kuma umarci duka jami'ai su gaggauta bayar da ko wane irin taimako ga wadanda suka samu raunuka."