Gwaninta ba ta karbi wani dan Nijeriya ba a Turai

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Wata karamar hukuma a arewacin Italiya ta soke wata tara da ta dora wa wani dan Najeriya dan cirani saboda yana share tituna ba tare da samun iznin hukuma ba.
'Yan sanda a Mestre da ke kusa da Venice ne suka ci tarar dan Najeriyar mai suna Monday kimanin $400.
To sai dai bayan da jama'a suka koka dangane da tarar, sai hukumomi suka amince cewa tarar ta yi yawa.
Tuni daman wani lauya a garin ya bude gidauniyar tara kudi domin biya wa Monday tarar.
Yanzu haka an amince za a bai wa Monday kudin tun da gwamnatin ta soke tarar da ta dora masa a baya.
Da dama daga cikin 'yan cirani 'yan Najeriya da ke Italiya sun gwammace su nemi taimakon jama'a maimakon yin roko ko bara.





