Mummunar girgizar kasa ta kashe mutum 19 a Pakistan

Bayanan bidiyo, Kalli bidiyon abin da ya biyo bayan girgizar kasa a Pakistan
An wallafa

Jami'ai a Pakistan sun ce wata girgizar kasa mai girman maki 5.8 ta afku a gabashin kasar, inda a kalla mutum 19 suka mutu wasu fiye da 300 kuma suka jikkata.

Lamarin ya faru ne a kusa da birnin Mirpur a yankin Kashmir da ke karkashin ikon Pakistan.

Hotunan da ake yadawa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda kwaltar da ke kan wani babban titi ta rufta, da kuma lalata gidaje.

Har yanzu ba a san girman barnar da girgizar kasar ta yi ba.

Dubban mutane ne suka mutu a wata mummunar girgizar kasa da ta afku a shekarar 2005.

Babban mai duba yanayin kasa na Pakistan Muhammad Riaz, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa,"Girgizar kasar ta kai zurfin kilomita 10... kuma a birnin Mirpur abin ya fi muni."

Rahotanni sun ce akwai yara cikin wadanda suka mutun.

People gather outside offices and shops in Mirpur, Pakistan-administered Kashmir. Photo: 24 September 2019

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Mutane da yawa mazauna Mirpur sun bar ofisoshinsu bayan da girgizar kasar ta afku saboda tsorata

Rundunar sojin Pakistan ta ce "an aika tawagar likitoci da sojin sama domin su kai agaji yankin."

Bayan girgizar kasar da ta afku a ranar Talata, an ji motsin kasa a wasu wuraren masu nisa da wajen kamar manyan biranen Pakistan da Indiya wato Islamabad da kuma Delhi.

Map