Mummunar girgizar kasa ta kashe mutum 19 a Pakistan

An wallafa

Jami'ai a Pakistan sun ce wata girgizar kasa mai girman maki 5.8 ta afku a gabashin kasar, inda a kalla mutum 19 suka mutu wasu fiye da 300 kuma suka jikkata.

Lamarin ya faru ne a kusa da birnin Mirpur a yankin Kashmir da ke karkashin ikon Pakistan.

Hotunan da ake yadawa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda kwaltar da ke kan wani babban titi ta rufta, da kuma lalata gidaje.

Har yanzu ba a san girman barnar da girgizar kasar ta yi ba.

Dubban mutane ne suka mutu a wata mummunar girgizar kasa da ta afku a shekarar 2005.

Babban mai duba yanayin kasa na Pakistan Muhammad Riaz, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa,"Girgizar kasar ta kai zurfin kilomita 10... kuma a birnin Mirpur abin ya fi muni."

Rahotanni sun ce akwai yara cikin wadanda suka mutun.

Rundunar sojin Pakistan ta ce "an aika tawagar likitoci da sojin sama domin su kai agaji yankin."

Bayan girgizar kasar da ta afku a ranar Talata, an ji motsin kasa a wasu wuraren masu nisa da wajen kamar manyan biranen Pakistan da Indiya wato Islamabad da kuma Delhi.