Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Buhari ya yi kwaskwarima a majalisar ministocinsa
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya yi garambawul ga majalisar ministocinsa kasa da wata biyu bayan rantsar da su.
Garambawul din ya shafi musayar ma'aikata ne tsakanin Karamin Ministan Neja Delta Festus Keyamo da kuma Senator Tayo Alasoadura shi ma karamin minista a Ma'aikatar Kwadago.
Mista Keyamo ne zai koma Ma'aikatar Kwadagon, inda shi kuma Senator Alasoadura zai koma ta Niger Delta, dukkaninsu a matsayin kananan ministoci.
Wannan bayani na kunshe ne a wata sanarwa da daraktan yada labarai na ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha ya fitar.
Willie Bassey ya ce wannan sauyi zai fara aiki ne nan take wato ranar Talata 24 ga watan Satumbar 2019.
Tuni Festus Keyamo ya gode wa shugaban kuma har ya halarci sabuwar ma'aikatar tasa, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.