Me 'yan Najeriya ke cewa kan sa dan gwamna makarantar gwamnati?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Tun dai ranar Litinin lokacin da gwamnan jihar Kaduna, Nasir Elrufa'i ya wallafa a shafinsa na twitter cewa ya sa dansa a makarantar gwamnati, 'yan kasar ke ta tattauna batun a kafar twitter.

Gwamna Elrufa'i dai ya bayyana cewa Abubakar Al-Siddique El-Rufai ya shiga aji daya na firamare Kaduna Capital.

Da ma dai gwamna Nasir Elrufa'i ya sha alwashin sanya dan cikinsa a makarantar gwamnati tun lokacin yakin neman zabe.

Kuma tun hawansa a 2015 ya fara daukar wasu matakan 'gyara' a tsarin ilimin firamare da sakandare a jihar, al'amarin da bai yi wa wasu 'yan jihar dadi ba.

Me jama'a ke fadi?