Boko Haram: Sojojin Najeriya sun yi galaba a fafatawa

Sojojin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sojoji uku ne suka rasu a artabun
An wallafa

Rundunar sojojin Najeriya ta ce rundunarta ta Operation Lafiya Dole ta yi wa mayakan kungiyar Boko Haram "mahangurba" a yayin wani rangadi bayan da suka yi arba da su a yankin da ya hada Monguno da Mairari da Gajiram na jihar Borno.

A wata sanarwa da ya fitar, mai magana da yawun rundunar Kanar Sagir Musa ya ce sojojin sun kashe da dama daga 'yan kungiyar yayin da wasu kuma suka tsere da raunuka a ranar Juma'a.

"Sai dai uku daga cikin dakarunmu sun rasa ransu wasu takwas kuma suka samu raunuka. Ana ci gaba da kula da wadanda suka samu raunukan," in ji Sagir Musa.

Ya kara da cewa rundunar ta kwace makamai masu yawa kuma har yanzu tana ci gaba da sintiri a yankin domin kakkabe 'yan Boko Haram.

'Abin da na gani da idona'

Tun a ranar Juma'a wani mazaunin garin Marte ya shaida wa BBC abin da ya gani da idanunsa, inda ya ce yana kyautata zaton bam ne ya tashi da motar sojojin guda daya.

"Mun yi mun ga mota uku kirar TATA cike fal da sojoji a kusa da wani kauye da ake kira Gasarwa, inda suka fito daga garin Munguno mu kuma tamu motar tana shiga garin na Mungona.

"Shigarmu Munguno ba jimawa sai kawai muka ga motoci na shigar da gawar sojoji masu yawa cikin barikin soji na Mai Malari da ke garin na Munguno.

"Bayan fitowarmu daga Munguno sojoji sun tsare mu sun bincika motarmu kafin su ba mu iznin wucewa.

"Da muka karasa Gasarwa dai-dai wurin da muka gan su lokacin da muke shiga Munguno sai muka sake ganin wadannan motocin guda uku kirar TATA an yi fata-fata da su kuma ba kowa a ciki.

"Ina kyautata tsammanin daya daga cikin motocin bam ne ya tashi da ita."

Wannan hari dai na zuwa ne kasa da mako biyu da kungiyar Boko Haram ta kai wasu hare-hare a garuruwan Konduga da Gubio da Magumeri na jihar Borno.

Rahotonni sun ce mayakan Boko Haram ne wadanda ke biyayya ga kungiyar IS wato ISWAP suka kai hare-haren.

An samu asarar rayuka da jikkata da ma asarar dukiya bayan da maharan suka cinna wa shaguna da gidaje da wasu gine-ginen gwamnati wuta.