Yadda wasu kasashe suka damu da abin da ke faruwa a Sudan

An wallafa

Gwamman mutane ne aka harbe yayin da kuma jami'an tsaro ke sintiri kan titi suna duka da harbin fararen hula suna cin zarafinsu.

Akalla mutum 113 aka kashe a rikicin Sudan tun lokacin da gwamnati ta bayar da umurnin tarwatsa 'yan adawa a ranar 3 ga Yuni, a cewar likitoci da ke da alaka da 'yan adawa.

Gwamnatin kasar ta amsa cewa mutum 46 aka kashe.

Amma abin da ke faruwa a Khartoum, na kara zama damuwa ga wasu gwamnatocin manyan kasashen kamar Riyadh da Alkahira da Ankara da Moscow.

Wakilin BBC a sashen Arabic Omar El Tayeb ya bayyana yadda wasu kasashe suke damuwa da rikicin Sudan da kuma yadda za su yi tasiri ga ci gaban rikicin.

Saudiya-Daular Larabawa-Masar

Abubuwan da ke tasiri a rikicin sassan gabas ta tsakiya, na taka rawa a Sudan. Musamman a daya gefen rikici tsakanin Saudiya da sauran kasashen tekun fasha a daya gefen kuma da Turkiya da Qatar.

Saudiyya da Daular Larabawa da Masar da ke makwabtaka da Sudan sun ba hukumomin sojin Khartoum goyon baya sosai.

Dukkanin kasashen sun fuskanci kalubalen bore, musamman na kungiyar 'yan uwa musulmi ta Muslim Brotherhood, wadanda suke ganin babbar barazana ce ga mulkinsu na danniya.

Gwamnatin Riyadh da Abu Dhabi sun samarwa sojojin tallafi, inda suka yi alkawalin bashin dala biliyan uku domin taimakawa Sudan farfado da darajar kudinta da kuma biyan kudaden shigo da kayayyaki cikin kasar.

Kafin soma arangama da masu zanga-zanga farkon watan nan, manyan hafsoshin sojin Sudan sun kai ziyara Riyadh da Abu Dhabi, tare da samun goyon bayan gwamnatin Masar.

Dukkanin wadannan kasashen tasirinsu ya karu tun bayan hambarar da gwamnatin shugaba Omar al-Bashir a watan Afrilu.

Turkey and Qatar

Turkiya da Qatar kuma wani bangare ne da ke da kyakkyawar alaka da Khartoum.

Qatar ta zuba jari a fannin doma da samar da abinci a aminiyarta Sudan, yayin da Turkiya da Sudan suka kara dankon zumunci karkashin Erdogan da Al-Bashir.

Qatar na zuba jari a cikin aikin noma da abincin abinci na abokin tarayya na Afrika, yayin da Turkiyya da Sudan suka ga wani sulhu a karkashin Recep Erdogan da Al-Bashir.

A watan Maris din 2018, Qatar da turkiya suka sanya hannu kan yarjejeniyar dala biliyan hudu da Sudan.

A lokacin mulkinsa na shekara 30, Al-Bashir ya yi kokarin tafiya da ko wane bangare, inda a daya bangaren ya yi kawance da masu kaifin kishin Islama, wani bangaren kuma ya shiga kawancen Saudiyya wajen yaki da 'yan tawayen Houthi a Yemen.

A watan Maris din 2015 al Bashir ya kai ziyara Saudiyya, bayan ya yanke hulda da Iran inda ya rufe dukkanin cibiyoyin al'adu na Iran a sassan Sudan.

Amma hukumomin Sojin Sudan an bayyana cewa sun fi kusa da Sauddiya, musamman jagoran juyin mulki Janar Abdul Fattah Al Burhan da mataimakinsa Janar Mohamed Hamdan Dagalo.

Tarayyar Afirka

Babu daya daga cikin wadannan bangarori da suka nuna goyon baya ga 'yan adawa, ko nuna suna sha'awar tabbatar da mulkin demokuradiyya a Sudan.

Masu zanga-zangar sun kunshi gungun kungiyoyin fararen hula da kungiyoyin kwadago da 'yan adawa.

Sun samu goyon bayan kasashen yammaci da Tarayyar Afirka, wadanda suka dakatar da Sudan tare da gargadin daukar mataki idan har ba a mika mulki ga farar hula ba.

Amma Sojojin Sudan suna ganin suna da babbar madogara a Tarayyar Afirka - Masar, da ke shugabancin kungiyar.

Firaministan Habasha, Abiy Ahmed ya isa Khartoum a ranar Juma'a domin shiga tsakanin tattaunawa tsakanin bangarorin biyu.

'Yan adawar sun yi watsi da tayin tattaunawa, inda suka ce sojojin kasar sun saba yarjejeniyar farko da aka amince don haka ba za su taba yarda da su ba.

Rasha da China da kuma Amurka

Makwabtan Sudan na yunkurin sasantawa ne ba tare da sa yawun manyan kasashe ba kamar Amurka da Tarayyar Turai.

Ta hanyar wakilcin Saudiyya, Amurka ta yi matsin lamba ga Khartoum domin kawo karshen yin amfani da karfi kan masu zanga-zanga, amma gwamnatin Trump ba wani damuwa ta yi da rikicin Sudan ba.

A Watan Janairu ne kadai Amurka ta dage takunkumi kan Sudan kan ta'addanci da keta hakkin dan Adam lokacin rikicin Darfur a 1990.

Sojojin Sudan kuma sun nuna sha'awar neman goyon bayan Tarayyar Turai kan yaki da ta'addanci da kuma rage kwararar 'yan ci-rani zuwa Turai.

Daga karshe dai China da Rasha na neman samun maslaha ne a Sudan.

Rasha ta dade tana sayar wa da Sudan da makamai, har lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta haramta cinikin makamai a 2005.

Kuma akwai kamfanonin Rasha da dama a Sudan da ake aikin hako mai da zinari.