Al-Nassr na son Diaz, Chelsea ta shiga neman Gyokeres, Massimiliano zai koma Milan

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Al-Nassr na son siyan dan wasan Liverpool Luis Diaz, Bayern Munich na da kwarin guiwar siyan Florian Wirtz, Chelsea na iya rike Jadon Sancho na Manchester United a yarjejeniyar dindindin.

Kungiyar Al-Nassr ta gasar Saudiyya na neman dan wasan Liverpool Luis Diaz, mai shekara 28, kuma tana bibiyar halin da kwantiragin dan wasan na Colombia ke ciki a Anfield. (Telegraph)

Zakarun Bundesliga Bayern Munich har yanzu suna da kwarin gwiwar shawo kan dan wasan Bayer Leverkusen Florian Wirtz, mai shekara 22, ya koma kungiyar a bazara, maimakon Liverpool (SZ Germany)

Chelsea ta gamsu da rawar da Jadon Sancho ya taka a baya-bayan nan kuma za su iya zuba zunzururutun kudi har fan miliyan 25 don siyan dan wasan na Manchester United a kwantiragin dindindin. (i Sport)

Brentford na tattaunawa da Liverpool kan yarjejeniyar sayen golan Jamhuriyar Ireland Caoimhin Kelleher, mai shekara 26. (Sky Germany)

Liverpool na son sama da fam miliyan 20 kan Kelleher. (Athletic)

Napoli na gab da kulla yarjejeniya da dan wasan Lille dan kasar Canada Jonathan David, mai shekara 25, wanda itama Juventus ta tuntube shi. (Sky Sports)

Chelsea ta bi sahun Juventus wajen yin wani bincike a hukumance da Sporting Lisbon kan batun neman dan wasan gaban Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 26, wanda itama Arsenal ke nema. (Record Portuguese)

Juventus na sha'awar sayen dan wasan gaban Real Madrid dan kasar Brazil, Endrick, mai shekara 18, a matsayin aro. (Calciomercato)

Tsohon kocin Juve Massimiliano Allegri na shirin komawa AC Milan a matsayin koci. Dan shekaru 57 ya shafe shekaru hudu a San Siro tsakanin 2010 da 2014. (Calciomercato)

Ipswich Town ta yi wa Chelsea tayin dan wasanta dan kasar Sipaniya, Marc Guiu, mai shekara 19 a matsayin aro a a gasar zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa. (Fabrizio Romano)