Man City na son Reijnders, Chelsea na harin Ekitike

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester City ta zage damtse kan farautar ɗan wasan tsakiya a AC Milan da Netherlands, Tijjani Reijnders, mai shekara 26, wanda aka kiyasta kuɗinsa kan £55m. (Mail)

Ɗan wasan tsakiya a Brazil, Casemiro mai shekara 33, da na Argentina Alejandro Garnacho, mai shekara 20, na cikin 'yan wasan da Manchester United ke son rabuwa da su a sabon kaka. (Telegraph - subscription required)

Manchester United ta tattauna da ɗan wasan Brentford da Kamaru, Bryan Mbeumo mai shekara 25, da aka yiwa kuɗi £50m. (Talksport)

Newcastle United na tattaunawa da ɗan wasan Ingila mai shekara 22, Liam Delap, a kokarin ganin sun shawo kan ɗan wasan na Ipswich ya dawo garesu maimako ya je Everton ko Manchester United ko Chelsea. (TeamTalk)

Newcastle ta nuna sha'awar saye ɗan wasan gaba a Brighton da Brazil, Joao Pedro mai shekara 23. (i Paper - subscription needed)

Chelsea ta tattauna da Eintracht Frankfurt kan ɗan wasanta mai shekara 22 daga Faransa, Hugo Ekitike. Hakazalika suna zawarcin ɗan wasan Sweden da ke taka leda a Sporting, Viktor Gyokeres mai shekara 26, da Delap na Ipswich. (Independent)

Eintracht Frankfurt ta yi wa ɗan wasan da Chelsea ke so Ekitike kudi a kan £84m. (Athletic)

Ɗan wasan Sunderland mai shekara 19 da ke buga tsakiya, Jobe Bellingham ya je Jamus inda yake tattaunawa da Eintracht Frankfurt - kwana biyu da taimakawa ƙungiyarsa. Borussia Dortmund - inda ɗan wasan Jude ke taka leda - da Leipzig duk sun kwaɗaitu da ɗan wasan. (Sky Sports)

Manchester United na son ɗan wasan Wolves da Portugal, Nelson Semedo. Ɗan wasan mai shekara 31kwantiragin da ya ke kai zai kare a wannan kakar. (Football Transfers)

Daraktan wasanni a Bayer Leverkusen, Simon Rolfes ya tabbatar da burin Liverpool na mallakar ɗan wasan Jamus mai shekara 22, Florian Wirtz. (Sky Sport Germany - in German)

Daraktan wasanni a Napoli, Giovanni Manna ya ce suna ta tattaunawa kan cimma yarjejeniya da ɗan wasan tsakiya a Belgium, Kevin de Bruyne, mai shekara 33. A wata mai zuwa kwantiraginsa ke karewa a Manchester City. (Rai News - in Italian)

Chelsea da Bayern Munich da Manchester United sun kwaɗaitu da ɗan wasan gaba a AC Milan da Portugal, Rafael Leao mai shekara 25, a wannan kaka. (Teamtalk)

Newcastle na duba yiwuwar tsawaita zaman ɗan wasanta na Ingila mai shekara 33, Callum Wilson. (Athletic - subscription needed)

Ƙungiyar Ligue 1 Paris FC na son cimma yarjejeniya da dan wasan Senegal mai shekara 35, Idrissa Gueye, wanda kwantiraginsa ke karewa a Everton a watan gobe. (Foot Mercato - in French)