Kane ya ci kwallo uku rigis karo na hudu a Bundesliga

Harry Kane

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Harry Kane ya zama na farko da ya ci kwallo uku rigis karo na hudu a kakar farko da yake buga Bundesliga.

Ranar Asabar Bayern Munich ta caskara Mainz 05 da cin 8-1 a wasan mako na 25 a babbar gasar tamaula ta Jamus.

Ke nan Bayern Munich ta rage tazarar maki, ya koma saura bakwai tsakaninta da Bayern Leverkusen, wadda ke jan ragama.

Watakila tazarar maki ya koma 10 da zarar Leverkusen ta yi nasara a kan Wolfsburg ranar Lahadi.

Bayan da Kane ya zura uku rigis a karawar, sauran da suka ci kwallayen sun hada Thomas Mueller da Jamal Musiala da Serge Gnabry da kuma Leon Goretzka da ya ci biyu.

Kane mai shekara 30 dan wasan tawagar Ingila ya ci kwallo 30 a wasa 25 a Bundesliga a kakar nan.

Kafin fara kakar nan Kane ya koma Bayern Munich daga Tottenham kan fam miliyan 90.

Bayern Munich na fatan lashe Bundesliga na 12 a jere, sai dai kamar da wuya a bana, bayan da Bayern Leverkusen wadda Xabi Alonso ke jan ragama take jan ragamar teburi da tazarar maki bakwai.