Tsohon kociyan Super Eagles Yusuf zai horar da Barau FC

Asalin hoton, Barau FC
Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Barau FC ta sanar da ɗaukar tsohon kociyan Super Eagles, Salisu Yusuf a matakin sabon wanda zai horar da ita.
A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar daga jami'in yaɗa labaran, Ahmad Hamisu Gwale ta ce kociyan ya ratta hannu kan yarjejeniyar kaka ɗaya a gaban shugaban Barau FC, Jakada Ibrahim Shittu Chanji.
Barau FC ta ɗauki Yusuf ne, saboda da ƙwarewa da gogewar da yake da ita a tamaula, domin ya kai ƙungiyar Premier League ta Najeriya daga gasar rukunin farko wato Nigerian Natinal League a kaka mai zuwa.
Yusuf ya horar da ƙungiyoyi da dama ciki har da Kano Pillars da Enyimba da El-Kanemi Warriors da kuma Enugu Rangers, ya san gasar tamaula ta kasar ciki da waje.
Haka kuma ya yi mataimakin kociyan tawagar Najeriya karkashin Stephen Keshi daga baya ya karbi aikin riƙon kwarya, wanda daga baya aka damƙa masa jan ragamar Super Eagles a Oktoban 2021.

Asalin hoton, Barau FC
Shi ne ya ja ragamar Super Eagles ta ƴan wasan da suke taka leda a gida har zuwa karawar karshe a gasar cin kofin Afirka da ake kira CHAN a 2018 a Morocco.
Barau FC na shirin tunkarar gasar tamaula ta Najeriya ta ƴan rukunin farko da ake kira NNL, za kuma ta kara a gasar atisayen tunkarar kakar gaba a Gusau/Ahlan Cup da za a yi a birnin Jos a jihar Plateau a watan nan.
Ƙungiyoyi 16 ne za su fafata a Jos a bana da suka ƙunshi daga Premier League da waɗanda za su kara a gasar rukunin farko.
Ana sa ran ƙungiyoyin za su halarci jihar Plateau ranar 19 ga watan Agusta, inda za a raba jadawali a ranar, sannan a fara wasa ranar 20 ga Agusta a Stadium Zaria Road a Jos a jihar Plateau.










