Kenya na son hadakar karbar bakuncin Gasar kofin Afirka a 2027

Asalin hoton, Getty Images
Kenya na shirin hadakar karbar bakuncin Gasar Cin Kofin Afirka a 2027 tare da wata kasa daga Kudancin Afirka.
Gwamnatin Kenya ta tsara gagarumin shirin da zai kai kasar ta samu gurbin shiga Gasar Kofin Duniya a karon farko a wanda za a yi a 2030.
Tawagar da ake kira Harambe Stars ta buga Gasar Kofin Afirka karo biyu tun daga 1993, an kuma dakatar da ita shiga wasannin 2023, bayan da Fifa ta hukuntata.
Sai dai kuma hukumar kwallon kafar duniya, Fifa ta janye takunkumin da ta dora mata.
Kenya na bukatar gina sabbin filaye da wuraren da zai sa a bata izinin karbar bakuncin babbar gasar tamaula ta Afirka.
Filaye shida Kamaru ta yi amfani da su a 2021, yayin da fili daya Kenya take da shi da hukumar kwallon kafar Afirka ta amince da inganshinsa.
Shi ne filin wasa da ake kira Nyayo National Stadium da ke babban birnin Nairobi.
Wasu kasashen da ake ganin Kenya za ta iya hadaka da su Gasar Kofin Afirkan sun hada da Uganda ko Tanzaniya, amma gwamnatin Kenya bata ce komai ba.
Tun farko Botswana da Namibia sun sanar da aniyar karbar bakuncin wasannin 2027 a Gasar Kofin Afirka.
Har yanzu CAF na kokarin zabar kasar da za ta karbi bakuncin fafatawar 2025, inda aka tsayar da ranar 16 ga watan Disamba don mika takardun neman izini.
Tun farko Guine aka bai wa izinin karbar Gasar 2025 daga baya aka karbe, bayan da kasar ke karancin filaye da kasa gina sabbi da wasu gine-gine don shirin wasannin.
A watan jiya Ivory Coast ta kammala sa hannu da CAF kan wasannin da za a buga a 2023, wanda za a kara a farkon 2024.









