City da Chelsea da Liverpool na gogayya kan Rigg, Fofana na son komawa Marseille

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester City, da Chelsea da kuma Liverpool na sha'awar matashin ɗan wasan tsakiya na Sunderland Chris Rigg na Ingila mai shekara 17. (Givemesport)

Ɗan wasan tsakiya na Ingila da Lille Angel Gomes shi ne babban wanda Newcastle take son saye amma kuma Liverpool, da Tottenham da Borussia Dortmund su ma suna son ɗan wasan mai shekara 24. (Sun)

West Ham na shirin karɓar tayi daga Galatasaray a kan ɗan bayanta na Italiya Emerson Palmieri. (Football Insider)

Ɗan bayan Faransa Wesley Fofana, mai shekara 23, ya ce yana tunanin barin Chelsea domin ya koma ƙungiyar garinsu Marseille a bazaran nan. (Free Foot)

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Ingila ta tattauna da wasu masu horarwa da dama duk da ƙoƙarin da Lee Carsley ke yi a matsayin kociyan riƙon ƙwarya na Ingila. (Telegraph)

Tsohon kociyan Ingila Gareth Southgate, mai shekara 54, ya ce watakila aikinsa na gaba ya kasamnce ba na ƙwallon ƙafa ba ne. (Sky News)

Mauricio Pochettino, zai riƙa karɓar albashin da ya kai dala miliyan 6 a duk shekara a matsayin kociyan Amurka. (ESPN)

Fifa na tattaunawa domin ƙara yawan ƙasashe a gasar kofin duniya ta mata zuwa 48 a shekara ta 2031, kamar yadda ake yi a gasar maza. (Telegraph)

Har yanzu Chelsea da Tottenham na son matashin ɗan bayan Lecce, Patrick Dorgu mai shekara 19 ɗan Denmark wanda aka yi masa kuɗi kusan yuro miliyan 40 (La Gazzetta dello Sport daga SportWitness)

Tottenham, da Newcastle da Arsenal na kan gaba a masu neman sayen ɗan gaban Lille, Jonathan David, ɗan Kanada to amma Juventus ma na so. (TuttoJuve)

Chelsea na son ɗan bayan Monaco da Brazil Vanderson, mai shekara 23, to amma Manchester United da Tottenham ma na cikin masu sonshi. (Caughtoffside)