Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real Madrid za ta je Sociedad buga La Liga ranar Lahadi
Real Madrid na shirye-shiryen zuwa Real Sociedad, domin buga wasan mako na biyar a La Liga ranar Lahadi 15 ga watan Satumba da za su kara a Reale Arena.
Tuni ƴan wasa suka fara kowama ƙungiyoyinsu, bayan buga wa tawagoginsu ko dai Nations League ko na neman shiga kofin duniya ko na Afirka ko sada zumunta.
Kociyan Real Madrid, Carlo Ancelotti ya samu yi wa Mbappe da Carvajal da Arda Güler da Brahim da kuma Valverde lale marhabin, bayan da suka koma sansanin ƙungiyar.
Da sanyin safiyar Laraba, Real ta yi atisaye, inda aka raba ƙwallo tsakanin ƴan wasa da yin bani in baka a tsakaninsu a ɗan karamin fili.
Ƴan wasa da ya haɗa da Alaba da Bellingham da Camavinga da Ceballos da Militão da kuma Tchouameni suna ta kokarin murmurewa daga jinya.
Real Madrid, wadda take ta biyu a teburin La Liga da maki takwas a bana, za ta je gidan Real Sociedad a wasan mako na biyar a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Daga nan ne Real mai Champions League a bara za ta karɓi bakuncin Stuttgard ranar Talata 17 ga watan Satumba a wasan farko a babbar gasar zakarun Turai ta bana.
Sai a ranar Asabar 21 ga watan Satumba, Real Madrid za ta kece raini da Espanyol a wasan mako na shida a La Liga a Santiago Bernabeu.