Ronaldo ya caccaki Ten Hag ya ce Man United na bukatar gagarumin sauyi

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Cristiano Ronaldo ya caccaki Erik ten Hag ya kuma ce Manchester United na bukatar gyara, kafin ta kalubalanci lashe kofuna nan gaba.

Kociyan ɗan kasar Netherlands na shan suka, bayan da United ta kare a mataki na takwas a teburin bara, ƙwazo mafi muni a Premier League.

A kakar bana da aka fara cikin watan Agusta, United ta ci Fulham, sai ta yi rashin nasara a Brighton da wanda Liverpool ta doke ta 3-0 a Old Trafford.

Ronaldo, wanda ya taka leda a Old Trafford karo biyu daga baya ya koma Al-Nassr ta Saudi Arabia, ya tambayi inganci da tunanin Ten Hag.

''Kociyan ya faɗa cewar ba za su iya lashe Premier League ba da Champions League a wata hira da ya yi da Rio Ferdinand, wadda za a watsa ranar Alhamis.

''A matakin kociyan Manchester United bai kamata ka ce ba za ka iya kalubalantar lashe Premier ko Champions League ba.

''Za ka iya cewa ba mu da dama, amma za mu sa kwazo don lashe kofunan.

''Fatan da nake yiwa Manchester United shi ne wanda nake yiwa kaina na fatan zama fitatciyar ƙungiya.

''Ina ƙaunar ƙungiyar ...Ni ba irin mutumin da zai mance baya bane.''

A kaka shidan farko da ya yi a United, Ronaldo ya lashe Premier League uku da Champions League da League Cup biyu da FA Cup da Fifa Club World Cup da Community Shield - daga nan ya koma Real Madrid a 2009.

Ya sake komawa United daga Juventus a Agustan 2021 da cin ƙwallo 145 a karawa 346 daga nan ya koma Al-Nassr a Disambar 2022.