Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 16/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 16 ga watan Yuni, 2026.

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Usman Minjibir

  1. Duk wani sabon harin Isra'ila kan Lebanon, saɓa yarjejeniya ne - Iran

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, ya gargadi cewa duk wani sabon hari da Isra’ila za ta kai kan Lebanon ko kuma ci gaba da mamaye yankuna a kasar, zai zama saɓawa yarjejeniyar da aka cimma da Amurka ne.

    Ya bayyana cewa Iran na kallon wannan yarjejeniya a matsayin dangantaka tsakanin Iran da kungiyar Hezbollah a gefe guda, da kuma Amurka da Isra’ila a gefe guda.

    Araqchi ya ce duk wani mataki da Isra’ila ta dauka sabanin wannan fahimta zai iya kara dagula al’amura a yankin, yana mai jaddada cewa Iran da abokan kawancenta za su dauki al’amarin da muhimmanci.

    Wannan gargadin na zuwa ne a daidai lokacin da tashin hankali ke kara kamari a yankin gabas ta tsakiya.

    Rahotanni sun nuna cewa Isra’ila ta sake kai wasu hare-hare a kudancin Lebanon, yayin da kungiyar Hezbollah ta sanar da cewa ta kaddamar da martani kan sojojin Isra’ila.

    Hakan ya kara tayar da hankulan jama’a kan yiwuwar barkewar sabon rikici a yankin.

    A nasa bangaren, Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya jaddada cewa sojojin kasarsa za su ci gaba da kai hare-hare a kudancin Lebanon, yana mai nuni da cewa Isra’ila ba za ta janye daga wadannan wurare ba duk da matsin lamba daga kasashen duniya.

    ity zones" in southern Lebanon will continue

  2. Sarkin Musulmi ya ayyana Talata 16 ga Yuni a matsayin 1 ga watan Muharram

    Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya ayyana ranar Talata, 16 ga watan Yuni, 2026, a matsayin 1 ga watan Muharram 1448, sabuwar shekarar Musulunci.

    Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga Majalisar Masarautar Sokoto.

    Sanarwar, wadda Farfesa Sambo Wali Junaidu, Wazirin Sokoto kuma shugaban kwamitin harkokin addini na majalisar masarautar ya fitar ta bayyana cewa wannan hukunci ya biyo bayan ganin jinjirin watan Muharram da kuma tabbatar da shi bisa ka’idojin addinin Musulunci.

    Watan Muharram shi ne farkon sabuwar kalandar Musulunci, wanda ke nuna fara sabuwar shekarar Musulunci.

    Haka kuma yana cikin watanni masu tsarki a Musulunci, kuma yana da muhimmanci wajen tunatar da al’ummar Musulmi game da hijirar Annabi Muhammad (SAW) daga Makka zuwa Madina.

    Sarkin Musulmi ya yi kira ga Musulmi a fadin Najeriya da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’o’i domin zaman lafiya, hadin kai da cigaban kasa, tare da karfafa imani da ayyukan alheri a sabuwar shekarar Musulunci ta 1448AH.

  3. An ji ƙarar fashewa a mashigar Hormuz da Qeshm

    An ji ƙarar wasu fashe-fashe guda uku a kudancin tsibirin Qeshm da kuma mashigar Hormuz a daren jiya kamar yadda Kamfanin dillancin labaran Mehr ya ruwaito.

    Jaridar ta ce fashe-fashen biyu na farko sun faru ne a daren Litinin, 15 ga watan Yuni, yayin da na uku ya faru da sanyin safiyar Talata, 16 ga Yuni.

    A cewar wakilin Mehr, fashe-fashen sun faru ne a cikin mashigar Hormuz, kuma rahotannin farko sun nuna hakan na iya faruwa ne domin sarrafa zirga‑zirgar jiragen ruwa a yankin.

    Sai dai har yanzu babu wata hukuma ta gwamnati a Iran da ta fitar da cikakken bayani kan lamarin, ciki har da rundunar juyin juya halin Iran IRGC ko hukumomin yankin.

    A wasu rahotanni makamantan haka, an taba alakanta karar fashewa a yankin da harbin gargadi ga jiragen ruwa da ke kokarin wucewa ba tare da izini ba, a lokacin da ake tsaurara matakan tsaro a mashigar Hormuz.

  4. Mutum takwas sun mutu a hatsarin jirgin yaƙin Amurka

    Mutane takwas sun mutu bayan jirgin yaƙin Amurka kirar B‑52 ya yi hatsari jim kaɗan bayan tashinsa daga wani sansanin soji da ke arewacin Los Angeles a ranar Litinin.

    Rahotanni sun nuna cewa jirgin ya tashi da misalin ƙarfe 11:20 na safe a lokacin da yake kan wani gwaji na yau da kullum, kafin ya faɗi ya kama da wuta.

    Hatsarin ya haddasa wata babbar guguwar hayaki wadda aka hango daga nesa yana tashi.

    Kanar James Hayes ya tabbatar da mutuwar duka mutanen da ke cikin jirgin, yana mai cewa:

    “Mun yi rashin ‘yan Amurka takwas masu muhimmanci,” inda ya ƙara da cewa hatsarin “ba zai yiwu a tsira ba.”

    Jami’an sansanin Edwards Air Force sun ce binciken farko ya nuna cewa ba za a iya kaucewa hatsarin ba ko ceto wasu ba, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano abin da ya haddasa shi.

    Jami’ai sun ƙara da cewa hatsarin ya faru ne a cikin yankin filin jirgin na sansanin, kuma an dakatar da zirga-zirgar jirage na ɗan lokaci domin gudanar da bincike da ayyukan ceto

  5. Trump ya musanta rahoton biyan Iran dala miliyan 300

    Shugaban Amurka Donald Trump ya musanta rahotannin da ke cewa kasarsa za ta biya Iran dala miliyan 300, inda ya bayyana hakan a matsayin “labarin ƙarya” a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social.

    Trump ya jaddada cewa Iran ta amince ba za ta mallaki makamin nukiliya ba, yana mai cewa yarjejeniyar da aka cimma tana da nufin hana hakan.

    Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance, ya bayyana a wata hira da manema labarai cewa Iran na iya samun fa’idodin tattalin arziki da suka kai biliyoyin daloli idan ta cika sharuddan da ke cikin yarjejeniyar.

    Sai dai ya ƙara da cewa akwai wasu muhimman sharuɗɗa da har yanzu ake tattaunawa a kai, kuma za a fitar da cikakken rubutun yarjejeniyar nan gaba.

    A gefen Iran kuwa, kwamandan rundunar Quds juyin juya halin Iran IRGC, Esmail Qaani, ya bayyana cewa sakamakon yarjejeniyar ya samo asali ne daga “tsayin daka” da ƙasar ta yi a yayin rikicin.

  6. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa barkanmu da ganin safiyar yau Talata

    A wannan shafin namu na kai tsaye, za mu kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na Facebook da X da kuma Whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.