Yan takara a Senegal sun buƙaci a yi zaɓe cikin mako 6

...

Asalin hoton, REUTERS

An wallafa

Ƴan takara 15 daga cikin 20 da aka amince su shiga zaben shugaban Ƙasar Senegal sun buƘaci da a gudanar da sabon zaƁen kafin ranar 2 ga watan Afirilu – ranar da ya kamata wa’adin mulkin shugaban Ƙasar na yanzu, Macky sally ya kare.

Ƴan takarar 15 sun kuma kafe cewa bai kamata a taɓa sunayen ba.

Ƙasar ta yammacin Afirka ta faɗa rikici ne bayan da Shugaba Salla ya sanar da ɗage zaɓen ƙasar, abin da kotun ƙolin ta ce ya saɓa doka.

Kasar ta Senegal da ke yammacin Afirka ta faɗa rikicin siyasa ne bayan kallon da ake yi mata da nuni a matsayin abar koyi a yankin wajen zaman lafiya da dumukuradiyya.

Shugaba Macky Sall yana son jinkirta zaɓen shugaban ƙasar ne da watanni da dama, kamar yadda ya ce domin sasanta rikicin cancantar wasu yan takarar.

Majalisar dokokin kasar ta amince da matakin shugaban inda ta ɗage zaben da ya kamata a yi a watan nan na Fabarairu zuwa watan Disamba.

Sai dai wannan mataki na shugaban ya gamu da cikas bayan da babbar kotun tsarin mulki, wato kotun ƙolin kasar ta ce ɗage zaɓen ya saba wa tsarin mulki.

A kan hakan ne kuma shugaban ya sauya matsaya inda a yanzu ya ce za a gudanar da zaben ba da jimawa ba.

A game da hakan ne yanzu waɗannan ƴan takara 15 daga cikin 20 da aka amince su shiga sabon zaben suke neman lalle a gudanar da zaben kafin ranar biyu ga watan Afirilu ranar da Shugaba Macky salla ya kamata ya sauka daga mulki, bayan wa’adinsa na ka’ida biyu.

A sanarwar da ‘yan takarar suka fitar wadda ta kunshi sa hannun wasu daga cikin na aba-gaba cikin ‘yan takarar ciki har da Bassirou Diomaye Faye, wanda aka tsare a kan zargin laifin angiza jama’a tayar da fitina, da kuma tsohon magajin garin babban birnin kasar, Dakar Khalifa Sall, ‘yan takarar sun bukaci da kada a taba jerin sunayen – ta hanyar soke sunayen wasu.

Ana ganin hukuncin kotun kolin kasar, na taka birki ga aniyar shugaban kasar ta jinkirta zaben har zuwa tsakiyar watan Disamba, ya sake dora ta kan turbar dumukradiyya da ta nemi ta baude, bayan zanga-zangar tsawon mako biyu da ta jefa kasar cikin yanayi na rashin tabbas.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A lokacin da Shugaba Salla ya sanar da aniyarsa ta dage zaben a ranar uku ga watan Fabarairu, ‘yan sa’o’I kafin a fara yakin neman zabe, ya bayar da hujja ta zargin kotun kolin da rashawa a matsayin daya daga cikin dalilan da ba za a gudanar da zaben a ranar 25 ga watan nan na Fabarairu ba, kamar yadda aka tsara.

Jam’iyyar shugaba Sall tare da ta daya daga cikin manyan ‘yan hamayyarsa, Karim Wade – sun zargi kotun kolin da cin hanci da rashawa, ‘yan kwanaki a baya.

Suna martani ne a kan kin sanya sunan Mista Wade, daga cikin ‘yan Takara, bisa daliin cewa yana da shedara takardar zama dan kasa biyu – ta Senegal da kuma Faransa, a lokacin da ya sanar da tsayawa Takara, abin da shi Mista Wade din ya musanta.

Wasu na ganin rikicin siyasar kasar na yanzu ya fara ne tun daga wannan lokaci da kotun kolin ta hana sanya sunan Mista Wade da sauran ‘yan hamayya a cikin wadanda za su tsaya takara.

To amma kasaancewar ita kuma kotun kolin ya yi wani hukuncin wanda ya saba Muradin shugaban kasar, na neman jinkirta zaben, abin da bai yi masa dadi ba, fargabar da ake yi ta cewa kasar ta kama hanyar zama ta mulkin karfa-karfa, hukuncin nata ya nuna cewa lalle fa har yanzu doka na aiki a kan kowa.

Shugaba Salla ya gamu da matsin lamba daga ciki da wajen kasar a kan ya sauya shawarar da ya yanke ta dage zaben.

Jiga-jigan ‘yan hamayya tare da shugabannin addinin MUsulunci masu tasiri sun solki lamirin shugaban.

Al’ummar Senegal na alfahari da kasancewar kasarsu a matsayin wadda tsarin dumukuradiyya ya zauna daram, kuma da yawa daga cikinsu suna ganin aniyar shugaban ta jinkirta zaben tamkar cin amana ne.

Ganin yadda a yanzu kasashe hudu a yankin Afirka ta Yamma, da Senegal din take, suna karkashin mulkin soja ne, kasashen duniya ke yi wa kasar kallon daya daga cikin ‘yan kalilan din da ke zama ababen koyi inda dumukuradiyya ke wanzuwa.

Duk da wannan suna da kasar ta yi a dumukuradiyya a idan aka kwatanta ta da sauran kasashe na yankin, lokacin mulkinsa ya gamu da zargi na take hakkin dan’adam, da ya hada da hana jama’a bayyana albarkacin bakinsu da kuma hana taruka.