Ɗage zaɓen Senegal ya saɓa wa ƙundin tsarin mulkin ƙasar - kotu

Asalin hoton, reuters
Matakin ɗage zaben da aka yi a ƙasar Senegal a wannan wata ya saɓawa kundin tsarin mulkin kasar, kamar yadda babbar kotun kasar ta yanke hukunci.
Majalisar tsarin mulkin ƙasar ta soke dokar shugaban kasar Macky Sall da kuma wani kudiri mai cike da cece-kuce da majalisar dokokin kasar ta amince da shi wanda ya mayar da zaɓen zuwa Disamba.
Sakamakon ɗage zaɓen ne aka gudanar da zanga-zangar da ta mamaye kasar da ke yammacin Afirka, wadda a da ake kallonta a matsayin tushen tsarin dimokiraɗiyya a yankin.
'Yan adawa dai sun ce hakan tamkar "yi wa dimokraɗiyya zagon ƙasa ne"
Mista Sall dai ya sanar da cewa zai ɗage zaɓen ne saboda nuna damuwa kan cancantar 'yan takarar adawa.
‘Yan majalisa 105 daga cikin 165 ne suka goyi bayan shawarar tasa bayan wata zazzafar muhawara da ‘yan sanda suka yi na cire wasu ‘yan majalisar adawa daga zauren majalisar.
Tun da farko dai an bada shawarar ɗage zaɓen da wata shida, amma gyaran da aka yi na karshe ya sa aka tsawaita ɗage zaɓen zuwa da watanni 10 wato 15 ga Disamban 2024 kenan.
Mista Sall ya nanata cewa ba ya shirin sake tsayawa takara. Sai dai masu sukar sa sun zarge shi da cewa ko dai yana ƙoƙarin maƙalewa kan ƙaragar mulki ko kuma yana yin rashin adalci ta hanayar yin tasiri ga duk wanda ya gaje shi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
'Yan takarar adawa da 'yan majalisar dokoki, waɗanda suka shigar da kararrakin shari'a da dama a kan kudirin ɗage zaɓen, sun ji kotun ta tabbatar da hukuncin da ya kamata a yammacin ranar Alhamis.
Khalifa Sall, babban ɗan adawa kuma tsohon magajin garin Dakar, babban birnin ƙasar, wanda ba shi da alaƙa da shugaban ƙasar ya kira ɗage zaɓen a matsayin "yi wa dimokraɗiyya zagon ƙasa".
Shi kuma Thierno Alassane Sall, wani ɗan takara wanda kuma ba shi da alaƙa da shugaban ƙasar ya kira ɗage zaɓen da "babban cin amanar ƙasa."
Kotun ta ce ba zai yiwu ba a gudanar da zaɓen a ranar 25 ga watan Fabrairu, nan da kwanaki 10 kacal kenan amma ta buƙaci hukumomi su shirya shi da wur-wuri.
Yawancin 'yan takara ba su yi yaƙin neman zaɓe ba tun lokacin da Shugaba Sall ya ba da umarninsa a ranar 3 ga watan Fabrairu, sa'o'i kafin a fara yaƙin neman zabe.
Matakin dai ya zo ne a daidai lokacin da aka sako wasu ‘yan siyasa na adawa da kungiyoyin farar hula daga gidan yari, lamarin da wasu a ƙasar ke kallo a matsayin wani mataki na farantawa jama’a rai.
An dade ana kallon Senegal a matsayin daya daga cikin ƙasashen da ke da kwanciyar hankali a tsarin demokraɗiyya a yankin.
Senegal ce kasa daya tilo a yankin yammacin Afirka da ba ta taɓa yin juyin mulkin soja ba.
Kasar ta kuma samu miƙa mulki sau uku cikin kwanciyar hankali inda har zuwa farkon wannan watan ba ta taba jinkirta zaben shugaban kasa ba.
Tun shekara ta 2012 ne shugaba Sall ke kan ƙaragar mulki, yayin da wa'adinsa na biyu zai ƙare a watan Afrilun 2024.

Asalin hoton, reuters











