Mainoo da Garnacho na iya barin Man United, Matheus Cunha kuwa na son barin Wolves

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Ƙofar Manchester United a buɗe take don cefanar da ɗanwasan Argentina Alejandro Garnacho, 20, da ɗanwasan tsakiya na Ingila Kobbie Mainoo, 19 a bazara. (Guardian).

Ɗanwasan gaba na Brazil Matheus Cunha, 25, ya zaƙu ya koma wata babbar ƙungiya duk da cewa ya sa hannu kan sabuwar kwantiragi da Wolves. (Football Insider).

Nottingham Forest ta yi fatali da tayin da Chelsea ta yi kan ɗanwasan Brazil Murillo, 22 a ranar ƙarshe ta cikar wa'adin kasuwar cinikayyar ƴanwasa. (Telegraph - subscription required).

Barcelona ta rasa samun fam miliyan 8.5 daga sayar da ɗanwasan Porto ɗanasalin Sifaniya Nico Gonzalez, 23 ga Manchester City saboda kulob ɗin na Portugal ya biya Barcelona fam miliyan 2.5 don rage yawan kuɗin cefanar da shi. (ESPN).

Ɗanwasan Manchester United Marcus Rashford, 27, ya yi watsi da tayin komawa wata ƙungiyar ƙwallon ƙafa taTurkiyya kafin ya koma Aston Villa a matsayin aro. (Manchester Evening News).

Rashford ka iya asarar kashi 100 na kuɗin tallafin da yake karɓa daga Nike saboda babban kamfanin da ke ɗinka kayan wasan ƴanƙwallo na kallon Aston Villa a matsayin ƙaramar ƙungiya a kan United. Nike na iya neman Rashford ya biya wani kaso cikin kuɗin cefanar da shi. (Mail Plus - subscription required).

Wasu ƴancikin gida na ganin za a iya kai wa shekarar 2032 kafin a kammala sake gina Old Trafford (Mail Plus - subscription required).

Akwai yiwuwar Newcastle United ta gina wani sabon filin wasa kusa da St James' Park. (Telegraph - subscription required).

United na son watsin da ta yi da tayin aro da Benfica ta yi kan ɗanwasa Tyrell Malacia, 25 ya zama ƙarshen sayar da ƴanwasa kan ƙa'idojin da ba su yi mata daɗi ba. (Mail Plus - subscription required).