Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man City ce kan gaba a yawan kashe ƙudi a Janairu
Manchester City ta kashe £180m wajen sayen sabbin ƴan wasa a Janairun nan, ita ce kan gaba a yawan kashe kuɗi tsakanin ƙungiyoyin Premier League.
Karo na biyu da aka kashe kuɗi da yawa a irin wannan lokacin, bayan da Chelsea ta sayi ƴan wasa kan £274m a 2023.
A tsakar daren Litinin aka kammala cinikayya a wasu kasuwar Turai da ta haɗa da ta Premier da La Liga da Bundesliga da Serie A da kuma Ligue 1.
Tun daga ranar 1 ga watan Janairu aka fara hada-hada, domin ƙungiyoyi su samu damar sayen ƴan wasa don kara musu karfin gwiwa a sauran wasannin bana.
A ranar Litinin City ta kammala ɗaukar ɗan wasan Porto, Nico Gonzalez kan £50m, hakan ya sa kungiyar Etihad ta kashe £180m jimilla.
Gonzalez shi ne na biyar da City ta saya a Janairun nan, wanda ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka huɗu.
Mai shekara 23 ɗan wasan tawagar Sifaniya, ya fara taka leda a kwararren ɗan wasa a Barcelona daga 2019 daga nan ya koma Porto a Yulin 2023.
Gonzalez ya ci ƙwallo tara ya bayar da tara aka zura a raga a wasa 68 a Porto da lashe babban kofin tamaula a Portugal a bara.
City wadda ke fuskantar kalubale a wasannin bana tana ta biyar ɗin teburin Premier League, bayan da Arsenal ta ɗura mata 5-1 ranar Lahadi.
Ƙungiyar Etihad mai rike da kofin Premier League tana da tazarar maki 15 tsakaninta da Liverpool ta ɗaya.
A Janairun nan City ta sayi ɗan wasan tawagar Masar, Omar Marmoush da na Brazil, Vitor Reis da na Uzbekistan, Abdukodir Khusanov da na Saliyo, Juma Bah.