Yadda sauyin yanayi ke sauya rayuwa har a duniyar wasanni

An wallafa

An soma aikin sake gina filin wasan Alexander a Fabarairun 2020 – wanda ya kasance cikin daminar da ba a taba ganin irinta ba a wata irin wannan a Burtaniya.

Aikin ya zo ƙarshe domin shiga shirye-shiryen gasar ƙasashen reinon Ingila a Yulin 2022, a daidai lokacin da yanayin ke sauyawa a sassan Burtaniya.

An shiga wani hali na sauyin yanayi. Sai dai kuma hakan abin ya ke a ko ina.

Kuma wasu daga cikin ƙasashen da ake fafatawa da su a Birmingham sun shaidi tasirin sauyin yanayin.

‘Yan tsere uku sun shaidawa BBC fargabarsu da fata kan makomar wasanni, bil’adama da kuma duniya.

Eliud Kipchoge (Dan tseren Kenya)

Kipchoge ya yi fice bayan kasancewa namijin farko da ya kamala gudun fafaliki a kasa da sa’o’I biyu a gasar da aka gudanar a Vienna a shekara ta 2019.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kipchoge ya yi fice bayan kasancewa namijin farko da ya kamala gudun fafalaki a kasa da sa’o’I biyu a gasar da aka gudanar a Vienna a shekara ta 2019.

"Inda nake zaune da gudanar da atisaye, can wani wuri ne a wajen garin Kenya, kusan kashi 80 cikin 100 na al’ummarsu manoma ne.

"Mutane sun fahimci cewa damina ta sauya ba kaman shekaru biyar baya ba, kuma yanayin ya sauya a zahiri.

"Ya na tasiri sosai kan masu wasannin motsa jiki. Sauyin yanayin ya munanan a wasu ƙasashen don haka akwai wahala mutum ya iya tseren sa’a biyu zuwa uku.

"Abin akwai takaici musamman ga mai gudun fafalaki.

"Tsere a wuri mai zafin gaske na da wuya. Akwai ban tsoro, ganin bayan kammala tsere sai mutum ya ji kamar duk ƙarfinsa ya ƙare.

"Mun shaida yada aka sauya lokacin tsere a gasar duniya da aka gudanar a Doha a 2019 cikin tsakiyar dare saboda tsananin zafi.

"Idan ka na son a fafata da kai, idan ka na son ka ji dadin tsere, dole sai yanayi ya kasance mai kyau da kuma iskar da za ka ke shaƙa.

"Don haka, yana da muhimmanci a gareni na fito na yi tsokaci kan yadda muhalli ke tasiri ga rayuwarmu.”

Eroni Sau (Mai wasan zari ruga a Fiji)

Sau na cikin tawagar Fiji da ta lashe azurfa a gasar Gold Coast ta 2018.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sau na cikin tawagar Fiji da ta lashe azurfa a gasar Gold Coast ta 2018.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

“Akwai babbar matsala, musamman inda na girma a tsibiri. A wannan wuri ka na iya ganin sauyin da yanayi ke haifarwa a kullum. Ya na faruwa a kan idanunmu.

"A garinsu mahaifiyata, akwai wani gini da ake amfani domin girki da wanka. Lokacin da na ke yaro tazarar ba ta wuce mita 10 ba da bakin teku. Amma a yanzu babu wannan gini.

“Abin da ka ke iya gani shi ne alamun gini a ƙarƙashin teku.

“Kwanan nan na koma gida bayan shafe shekara hudu ina balaguro. Akwai kabarin da muka binne kakannina, amma a yanzu mutane na maganar sauyawa gawawwakinsu wuri ko kusa da tsauninka saboda ƙarfin teku da ke mamaye ko ina.

“Yana shafar rayuwarmu sosai, harda ta wasanni.

"Muna yara burinmu shi ne wasanni zari ruga a bakin teku. Muna jindadin wasannin mu musamman ganin a gefe ga shuke-shuken bishiyun kwa-kwa.

“A yanzu ƙasar da ke taruwa bakin teku ba ta da yawa, ruwa ya shanye har inda ake da bishiyun kwa-kwa. Babu batun maganar bakin teku, babu wurin da za a iya wasa.

Mubal Azzam (Mai wasan ninkaya a Maldives)

Azzam na daga cikin wadanda suka wakilci Maldives a wasannin Olympics na Tokyo.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Azzam na daga cikin wadanda suka wakilci Maldives a wasannin Olympics na Tokyo.

“A tsiribai da dama a Maldives, ambaliya ta cinye gidaje da dama sannan ana samun zabtarewar ƙasa.

“A birnin Male, inda kusan nan nayi rayuwata, akwai bakin tekun da mutane ke zuwa, amma a yanzu an samu sauye-sauye saboda babu ƙasar tekun, sannan wuraren na ta zabtarewa. Komai fa ya sauya.

“Muna ganin yada rayuwar mutane a wasanni ke sauyawa  a yanzu. Muna ganin tasirin haka a zahiri.

“Ni da abokai na kan shiga teku domin atisaye, amma a yanzu a galibin lokuta hakan na gaggara saboda ruwan a galibin lokuta ya gurbace.

“Amma mun san cewa dole mu yi amfani da shi saboda babu abin da zamu iya yi. Amma hakan na sa ni tunanin yadda zan iya taimakawa ƙasata da mutane domin kare muhalli.

“Ina ganin akwai abin da mutane za su iya yi domin kawo sauyi musamman a duniyar wasanni.

“Na sha gamuwa da mutane da ke da kishin hakan. Ina ganin wasanni na da tasiri, domin akwai tasirin da suke yi a duniya.”