Liverpool na zawarcin Alonso, Arsenal da Man U da Chelsea na son Ramaj

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ta gabatar da bukatar farko ta tattaunawa da kocin Bayer Leverkusen Xabi Alonso yayin da take neman wanda zai maye gurbin Jurgen Klopp . (Bild - in German)
Tottenham na son ta inganta yawan ‘yan wasan gabanta, shi ya sa ta sayi dan wasan gefe na kungiyar Wolves da Portugal Pedro Neto, dan shekara 23 da kuma dan wasan gefe na Crystal Palace da Ingila Eberechi Eze, mai shekara 25, (Independent)
Manchester United za ta yanke shawara a kan makomar dan wasan gaba na Ingila Mason Greenwood dan shekara 22 wanda a halin yanzu an ba da shi aro ga Getafe,har zuwa karshen watan Mayu. (Sun)
Arsenal da Manchester United da Chelsea na zawarcin mai tsaron gidan Jamus da Ajax Diant Ramaj, dan shekara 22 (Bild)
Watakila Everton ta sake yin nazari game da makomar dan wasan tsakiyarta da Ingila Dele Alli mai shekara 27 a karshen badi bayan da Toffees ta nuna alamun a shirye ta ke ta tattauna da shi a kan sabon kawantaragi (Express, via Athletic)
Dan wasan gaban Koriya ta Kudu Son Heung-min mai shekara 31, na son ya ci gaba da taka leda a Tottenham inda nan bada jima wa ba za su fara tattaunawa da juna a kan sabon kwantaragi. (Football Insider)
Watakila Liverpool ta yi amfani da damar da ta samu na daukar dan wasan gefe na kasar Kamaru da Brentford, Bryan Mbeumo dan shekara 24 wanda kungiyarsa ta koma mataki na kasa a wasan firimiya. (Express)
Barcelona na son daukar dan wasan gaban Portugal Rafael Leao dan shekara 24, sai dai ya ce ‘’ba ya son ya bar " AC Milan. (Sport - in Spanish)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dan wasan tsakiya na Italiya Jorginho, mai shekara 32, watakila ya koma Serie A bayan kwantaraginsa da Arsenal ya zo karshe a wannan bazara. (Goal)
Kungiyoyin kwallon kafa na Saudi Pro na zawarcin taurarin 'yan wasan firimiya da dama a kasuwar sayar da ‘yan wasa ta bazara da kuma matasa irinsu dan wasan gaba na Argentina Matias Soule dan shekara 20 wanda a halin yanzu Juventus ta ba da shi aro ga Frosinone . (ESPN)
Ita ma kungiyar Al Qadsiah ta yi wa tsohon dan wasan tsakiya na Sfaniya Sergi Roberto tayi mai tsoka ,sai dai kyaftin din Barcelona mai shekara 32 ya fi son ya koma MLS ta Amurka. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Brighton za ta karbi kudi mai yawa sosai a kan dan wasa mai shekara 14 bayan da wata kotu ta yanke hukuncin cewa dole ne Chelsea ta biya fam miliyan 4.25 a kan dan wasa Ingila mai kai hari a tawagar kasar ta masu shekaru kasa da 17 Shumaira Mheuka, wanda a halin yanzu shekararsa 16 amma a shekarar 2022 ne aka dauko shi. (Football Insider)
Michael Edwards zai so ya samu cikakken iko kafin ya amince da komawa Liverpool a matsayin daraktan wasanninta kuma watakila wannan ya sa daraktan fasaha na Bournemouth Richard Hughes ya bar kungiyar. (Mirror)











