An naɗa O'shea kocin riƙon ƙwarya na Jamhuriyar Ireland

O'Shea

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

An naɗa tsohon ɗan wasan bayan Manchester United John O'Shea a matsayin kocin rikon kwarya na Jamhuriyar Ireland.

O'Shea, mai shekaru 42, ya buga wa Jumhuriyar wasanni 118 tsakanin shekara ta 2001 zuwa 2018.

Ya taɓa zama mataimakin koci a karkashin kocin da ya gabata Stephen Kenny, kuma ya yi aiki da ƙungiyar 'yan ƙasa da shekara 21 ta ƙasar.

O'Shea ne zai jagoranci tawagar a wasannin sada zumunci da Belgium da Switzerland a watan Maris kuma mataimakin kocin Crystal Palace Paddy McCarthy zai mara masa baya.

Tsohon ɗan wasan bayan na Sunderland ya taɓa horar da ƙungiyar Reading da Stoke City kafin ya koma ƙungiyar Birmingham City bayan an naɗa tsohon abokin wasansa a Manchester United Wayne Rooney a matsayin koci.

Ya bar ƙungiyar ta gasar Championship a watan Janairu bayan da aka sallami Rooney a matsayin koci.

Hukumar kwallon kafa ta Jumhuriyar ta kuma tabbatar da cewa za ta naɗa kocin dindindin a farkon watan Afrilu.