FA Cup: Yadda za a kece raini a zagayen quater-final

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City mai rike da kambun gasa za ta karɓi baƙuncin Newcastle United, yayin da Manchester United za ta kara da Liverpool.
United ta doke Nottingham Forest da ci 1-0 a wasan zagaye na biyar, yayin da Liverpool ta yi nasara kan Southamptonda ci 3-0 a wasannin da aka buga da yammacin laraba.
Tun da farko dai Chelsea ta doke Leeds da ci 3-2 a wasan farko da aka fafata kuma yanzu za ta karɓi baƙuncin Leicester a zagaye na gaba.
Coventry kulob ɗin da ke Championship, wanda ita ce matsayi mafi karanci da ta rage a gasar, za ta ziyarci Wolves.
An shirya gudanar da wasannin zagayen kwata fainal daga ranar Asabar 16 ga watan Maris.
Coventry, wacce ta dauki kofin a shekarar 1987, ita ce ta farko da ta kai matakin takwas na karshe lokacin da ta lallasa Maidstone da ci 5-0 ranar Litinin.
Newcastle ta sah da ƙyar a bugun fanareti a karawarta da Blackburn ranar Talata, yayin da Erling Haaland ya ci ƙwallo biyar yayin da Manchester City ta ta lallasa Luton da ci 6-2.
Jaddawalin wasannin quater-Final
Wolverhampton Wanderers da Coventry City
Manchester United da Liverpool
Chelsea da Leicester City
Manchester City da Newcastle United











