Abin da ya sa ba ma so mu koma gida — ‘Yan gudun hijira

Sau da dama hukumomi a Jamhuriyar Kamaru, tare da hadin gwiwar Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya kan shirya yadda za su mayar da wasu ‘yan gudun hijirar Jamhuriyar Tsakiyar Afrika gida bisa radin kansu.
To amma a wasu lokutan ‘yan gudun hijrar kan zabi su zauna a sansanonin da aka ajiye su ana kula da su maimakon su koma garuruwansu na asali.
Hakan kuwa na da nasaba da rashin tabbas din da yawancinsu ke cewa a game da batun tsaron wurarensu na asali.
A 2022 kaɗai, an gudanar da irin wannan shiri kusan sau shida a sansanoni ‘yan gudun hijra daban-daban, kamar misali sansanin Gado Badzere da na Lolo.
Yawancin ‘yan gudun hijrar da ke zaune a wadan nan sansani musamman mata sun zabi su ci gaba da zama a in da suke a maimakon a kwashe su a mayar da su garuruwansu na asali na suka bari saboda matsalar tsaro.
Wasu mata da BBC ta tattauna da su sun bayyana cewa su fa zamansu a wadan nan sansanoni yafi musu gida.
Hauwa’u Adamu, ‘yar gudun hijira ce daga Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, ta shaida wa BBC cewa, gaskiya ita ba zata koma gida ba saboda komawar akwai matsala don zaman lafiya bai gama zama ba.
Ta ce,” Akwai ‘yan uwana da yawa da aka kashe, ga asarar da muka yi, don haka koda mun koma ma wanne jin dadi za mu yi? duk ‘yan uwa an kashe su zan koma ne na zauna ni kadai?”
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Hauwa’u ta ce yawancin ‘yan uwanta da aka kashe ‘yan tawayen silika ne suka kashe su, gashi kuma sun kashe dukkan kadarorinsu kamar dabbobi da makamantansu.
‘Yar gudun hijirar ta ce, ita fa yanzu hankalinta ya fi kwanciya a wannan sansani domina na taimaka musu da abinci ga shi kuma suna ‘yan sana’oinsu na hannu kamar sayar da kayan miya da dinke-dinke.
Sannan kuma ‘ya’yansu na zuwa makaranta gashi kuma ba bu tashin hankali, don haka idan aka ce za a mayar da su garuruwansu na asali gaskiya basa so.
Maryam Isa, ita ma ‘yar gudun hijira ce daga Jamhuriyar Tsakiyar Afirka wadda ke zama a daya daga cikin sansanonin ‘yan gudun hijirar da ke Kamaru, ta ce sam ba za ta koma garinsu na asali ba saboda bata ma san in da za ta nufa idan ma taje.
Ta ce,” Ba mu da daki ballantana gida, don haka idan mun koma a ina zamu kwana da mu da yara?, rikicin da aka yi shi ya sa aka lalata mana gidajenmu.”
Maryam, ta ce a yanzu ta shafe shekaru bakwai tana zaune ita da ‘ya’yanta da jikokinta a sansanin ‘yan gudun hijira, kuma suna sana’arsu kamar sayar da kayan miya, gashi kuma ana ba su abinci, ‘ya’yansu kuma na zuwa makaranta.
Don haka idan muka ce zamu bari a kwashe mu a mayar da mu gida ta ina zamu fara? Ai gara mu ci gaba da zama a in da muke har sai gwamnatin kasarmu ta samar mana muhalli kafin mu koma gida, in ji ta.
Mutane da dama ne daga Jamhuriyar Tsakiyar Afirka suka fice daga kasarsu kusan shekara tara ke nan in da suke zama a kasashe daban daban, kamar Chadi da Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo da kuma Kamaru in da mafi akasarin ‘yan kasar suka fi zama a matsayin ‘yan gudun hijira.
Rikicin addini da na kabilanci tsakanin kungiyoyin masu rike da mukamai na silika da ke goyon bayan musulmai da na Anti Balaka, masu mara wa kiristoci baya ne ya sanya ficewar wadannan mutane daga kasarsu.










