Kasashe 10 da suka fi yawan ƴan gudun hijira a duniya

Habasha

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Yankin kudu da hamadar Saharar Afirka ne lamarin ya fi shafa
An wallafa

Mutum miliyan biyar ne suka rasa muhallansu a cikin ƙasar Ethiopia wato Habasha, adadi mafi girma ke nan na irin wannan 'yan gudun hirar, a cewar wani rahoto.

Rahoton na shekara-shekara daga Internal Displacement Monitoring Centre (IDMC) ya ambaci Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, da Afghanistan, da Myanmar da suka samu adadin 'yan gudun hijira na cikin gida a 2021.

Hakan ya sa adadin ya zama miliyan 59 na 'yan gudun hijirar a faɗin duniya tun daga ƙarshen shekarar da ta wuce musamman saboda ƙaruwar rikice-rikice.

An samu ƙarin fiye da miliyan huɗu cikin shekara ɗaya, a cewar rahoton.

Jadawalin 'yan gudun hijira

Asalin hoton, BBC

Wani rahoto da ƙungiyar da ke bin sawun 'yan gudun hijira ta Norwegian Refugee Council ta tattara ya ce yankin kudu da hamadar Saharar Afirka ne lamarin ya fi shafa.

A arewacin Habasha, yaƙin da aka shafe wata 18 ana yi ya haifar da rikici a rayuwar ɗan Adam, inda miliyoyin mutane suka fuskanci ƙuncin rayuwa.

Babu haƙiƙanin adadin waɗanda suka mutu sakamako yaƙin, wanda ke cike da cin zarafi da aika-aika da ƙungiyoyin kare haƙƙi ke cewa sun kai girman laifukan yaƙi.

Jadawalin 'yan gudun hijira

A yankin Tigraya na arewacin ƙasar da aka fara yaƙi Nuwamban 2020, miliyoyin mutane na cikin buƙatar taimako.

A sauran sassan ƙasar, adadin mutane da ba a saba gani ba na guduwa daga gidajensu saboda rikicin ƙabilanci da addini.

Jadawalin 'yan gudun hijira

Rundunar sojan ƙasar na shirin gudanar da wani samame kan 'yan tawayen yankin Orom da ake kira Oromo Liberation Army (OLA) - kuma ana fargabar zai iya haddasa mace-macen fararen hula da kuma sake ta'azzara halin ƙunci.