Man Utd na zawarcin Southgate, Barcelona na son Arteta

Asalin hoton, BBC Sport
Kocin Ingila Gareth Southgate da kocin Brentford Thomas Frank na daga cikin mutanen da Manchester United ta ke zawarci domin maye gurbin Erik ten Hag a karshen kakar wasa ta bana (ESPN)
Barcelona ta ci gaba da zawarcin kocin Arsenal Mikel Arteta domin maye gurbin Xavi, wanda zai bar kungiyar a karshen kakar wasa ta bana amma kungiyar ta Sfaniya ta san nadin nasa abu ne mai wuya. (Relevo - in Spanish)
Liverpool da Arsenal da Manchester City na son su dauko dan wasan tsakiya na Bayern Munich Joshua Kimmich. Dan wasan kasar Jamus mai shekara 29 na son ya bar Bavaria a wannan bazara. (Express)
Duk wata kungiyar kwallon kafa da ke son ta dauko kocin Brighton Roberto de Zerbi aiki a wannan bazara sai ta biya Seagulls fam miliyan 12. Barcelona da Liverpool da Manchester United dukkaninsu na zawarcin kasar Italiyar.(Mirror)
Bayern Munich ta sha gaban Liverpool a kokarin da su ke yi wajan nada Xabi Alonso a matsayin sabon kocinsu idan dan kasar Sfaniya ya amince ya bar Bayer Leverkusen a wannan bazara. (Telegraph - subscription required)
Liverpool na son ta nada Richard Hughes a matsayin daraktan wasanni bayan da dan shekara 44 ya tabbatar cewa zai bar aikinsa a Bournemouth a karshen kakar wasanni. (Times - subscription required)
Ana dai ganin Hughes zai iya zuwa Newcastle United,yayin da Frederic Massara,wanda shi ne daraktan kwallon kafa a AC Milan, a daraktan wasanni na Nice Florent Ghisolfi na cikin wadanda Liverpool za ta iya dauka. (Independent)
Liverpool da Borussia Dortmund da Paris St-Germain na sha’awar dan wasan tsakiya na kasar Argentina Alan Varela mai shekara 22 amma sai ta biya Porto fam miliyan 60. (Foot Mercato - in French)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dan wasan tsakiya na Brazil Joelinton na son ya ci gaba da kasancewa a firimiya idan dan wasa mai shekara 27 ya kasa cimma matsaya da NewCastle sabon kwantaragin da ya wuce shekara 2025. (Football Insider)
Chelsea na son ta dauko dan wasan gefe na Athletic Bilbao Nico Williams. Dan wasan gaban Sfaniya dan shekara 21 zai iya barin kungiyar a kan fam miliyan 43 a wannan bazara. (Telegraph - subscription required)
Arsenal na zawarcin Williams din da dan wasan gefe na Wolves da Portugal Pedro Neto dan shekara 23 da dan wasa mai kai hari na Brentford Ivan Toney mai shekara 27 (Evening Standard)
An yi wa West Ham tayin daukar dan wasan Borussia Dortmund da Jamus Marco Reues mai shekara idan wa’adin kwantaraginsa ya zo karshe a wannan bazara 34. (Football Insider)
Dan wasan tsakiya na Ajax Jordan Henderson mai shekara 33, bai yi nadama ba game da barin Liverpool yana mai cewa wannan shi ne ‘’mafi alheri’’ ga bangarorin biyu. (Guardian)












