Aston Villa ta yi asarar fam miliyan 119.6 a kakar wasan 2022-23

Aston Villa

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Aston Villa ta ba da rahoton asarar fam miliyan 119.6 a kakar wasanni da ta gabata a ranar 31 ga Mayun 2023.

Rahoton ya ƙunshi lokacin da Villa ta ƙare a matsayi na bakwai a gasar Premier inda ta samu cancantar shiga gasar UEFA Conference League.

Villa ta ce alkaluman sun yi daidai da tsarin kasuwancin ƙungiyar kuma ba ta keta ƙa'idojin ribar Premier League ba.

Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta ce: "Mamallakan Aston Villa na ci gaba da jajircewa wajen ganin an samu ci gaba mai ɗorewa a ƙungiyar, kuma muna fatan samun ci gaba wajen cimma abubuwan da mu ka sa a gaba."

Villa ta samu ribar Fam 300,000 a asusunta a kakar 2021-22, bayan ta sayar da ɗan wasan tsakiya na Ingila Jack Grealish ga Manchester City kan fam miliyan 100.

Ƙungiyar ta samu ƙaruwar kuɗaɗen shiga na fam miliyan 217.7 a shekarar 2022-23, daga fam miliyan 178.4 a shekarar da ta gabata.

Ta kashe fam miliyan 63.7 kan sabbin ƴan wasa da suka haɗa da Diego Carlos daga Sevilla kan farashin fam miliyan 26 da Philippe Coutinho daga Barcelona kan farashin fam miliyan 17, yayin da suka samu fam miliyan 22 daga sayar da ƴan wasa.

Ƙungiyar ta kuma kori kocinta Steven Gerrard inda ta maye gurbinsa da Unai Emery, wanda ya taimaka wa ƙungiyar ta kammala gasar lig a matsayi mafi kyawu tun 2009-10 kuma ta samu gurbin shiga gasar Turai a karon farko cikin fiye da shekaru goma.

A halin yanzu tana matsayi na huɗu a gasar Premier League kuma ta kama hanyar samun gurbi a gasar zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa.