An dakatar da Bellingham buga wasanni biyu

Asalin hoton, Getty Images
An dakatar da ɗan wasan Real Madrid Jude Bellingham na wasanni biyu a gasar La Liga saboda jan katin da ya samu a wasan da Real ta yi 2-2 da Valencia.
Bellingham, mai shekaru 20, ya yi tunanin ya zura ƙwallo a minti na shida na ƙarin lokaci kafin a tashi daga wasan da aka buga a filin wasan Mestalla ranar Asabar da ta gabata.
Sai dai alƙalin wasa Gil Manzano ya busa tashi kafin ƙwallon ta shiga da'ira ta 18.
Amma ɗan wasan na Ingila zai iya buga wasan da Real za ta yi da RB Leipzig a gasar cin kofin zakarun Turai ranar Laraba.
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Sifaniya (RFEF) ta ce Bellingham ya nuna " raini ko rashin ɗa'a " ga Manzano lokacin da ƴan wasan Real da ma'aikatansu suka kewaye shi.
Bellingham, wanda ke dawowa bayan shafe makonni uku yana jinya, zai kuma biya tarar Yuro 600.
Real ta ɗaukaka ƙara kan jan katin da aka bai wa Bellingham amma kwamitin ladabtarwa na RFEF ya yi watsi da hujjar cewa alƙalin wasan ya yi kuskure.
Ɗan wasan zai dawo gasar La Liga a wasan da Real za ta fafata da Athletic Bilbao a ranar 31 ga Maris bayan hutun wasannin ƙasa da ƙasa.











