Ana neman Fernandes a Saudiyya, Madrid ta dage kan Zubimendi, Arsenal na son Kang-in

Bruno Fernandes

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bruno Fernandes
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Bruno Fernandes na daukar hankalin Saudiyya, kungiyoyin Premier da dama na neman Harvey Elliott da, Arsenal ta sabunta neman Mohammed Kudus.

Al-Hilal na shirin neman kyaftin din Manchester United Bruno Fernandes, amma Red Devils din ba ta da niyyar siyar da dan wasan tsakiyar dan Portugal mai shekara 30. (Mail)

Newcastle na sa ido kan dan wasan Bayer Leverkusen mai shekaru 29 da dan wasan baya na Jamus Jonathan Tah, wanda zai bar kungiyar idan kwantiraginsa ya kare a bazara. (Sun)

Dan wasan tsakiya na Liverpool Harvey Elliott, mai shekara 22, yana jan hankalin kungiyoyin Premier da dama, ciki har da Wolves. (Talksport)

Real Madrid ba ta shirin zawarcin dan wasan tsakiya na Real Sociedad Martin Zubimendi saboda ba su bukatar dan wasan na kasar Sipaniyan, wanda farashinsa ya kai euro miliyan 60 (£51m). (OK Diario)

Dan wasan tsakiya na Italiya Jorginho, mai shekara 33, yana tattaunawa da kulob din Flamengo na Brazil game da komawarsa kungiyar a kyauta idan yarjejeniyarsa a Arsenal ta kare a karshen kakar wasa ta bana. (Mail)

Arsenal na tunanin sake komawa neman dan wasan tsakiyar Paris St-Germain Lee Kang-in, mai shekara 24, bayan da ta kasa kulla yarjejeniya da dan wasan na Koriya ta Kudu a watan Janairu. (Sun)

Dan wasan Bayer Leverkusen da Jamus Florian Wirtz, mai shekara 22, na shirin yin shuri da da batun komawa Manchester City da Real Madrid da Bayern Munich. da sukansu suke zawarcinsa (Bild)

Farashin dan wasan RB Leipzig Benjamin Sesko ya haura €80m (£68m) amma kungiyoyi za su iya siyan shi a kan kasa da hakan idan aka yi tayin da ya dace kan dan wasan na Slovenia mai shekaru 21. (Sky Sports Germany)

Arsenal na zawarcin dan wasan West Ham da Ghana Mohammed Kudus, mai shekara 24. (Talksport)

Federico Chiesa, mai shekara 27, zai iya barin Liverpool a wannan bazarar, yayin da AC Milan da Napoli ke zawarcin dan wasan na Italiya. (Calciomercato)

Manchester United ta saka golan Torino dan kasar Serbia Vanja Milinkovic-Savic, mai shekara 28 a cikin jerin 'yan wasan da za su nema a bazara. (Givemesport)