Inter Milan ta kai zagayen ƙarshe bayan doke Barcelona

Asalin hoton, Reuters
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1
Inter Milan ta kai zagayen ƙarshe bayan samun sa'ar Barcelona a wasan da suka yi ruwan ƙwallaye tsakaninsu.
An tashi wasan ne ci 4-3 a San Siro gidan Inter Milan bayan sun yi 3-3 a gidan Barcelona.
Lautaro Martinez da Hakan Calhanoglu suka fara ci wa Inter ƙwallo a ragar Barcelona, daga baya Eric Garcia da Dani Olmo da Raphinha suka rama ƙwallayen har da ƙari.
Francesco Acerbi ya rama wa Inter ƙwallo ta uku ana dab da tashi, wanda ya tilasta wasan zuwa ƙarin lokaci.
Frattesi ne ya ci wa Inter Milan ƙwallon da ya ba ta nasara.
Inter ta haramta wa Barcelona zuwa wasan ƙarshe karon farko bayan shekara 10.
Yanzu Inter Milan za ta haɗu ne da PSG ko Arsenal waɗanda za su fafata a ranar Laraba.







