Magoya bayan PSG na iya ruɗa Arsenal - Hakimi

Hakimi

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ɗanwasan baya na PSG Achraf Hakimi ya yi gargaɗi ga Arsenal ta shirya fuskantar hayaniyar magoya baya a karawa ta biyu da za su fafata a Parc des Princes ranar Laraba a gasar Zakarun Turai.

A bana PSG ta doke Manchester City da Aston Villa a gidanta, kuma ta fi yawan riƙe ƙwallo a fafatawar da Liverpool ta ci ta 1-0 a watan Maris.

Hakimi ya ce ya yi imanin magoya bayan PSG na da matuƙar muhimmanci wajen zaburar da su domin kare nasararsu kan Arsenal.

PSG ta tafi gidan Arsenal ta ci ta 1-0 a Emirates. Dole Arsenal ta rama da ƙoƙarin doke PSG domin zuwa zagayen ƙarshe a gasar.

Hakimi ya ce, "yanayi ne na daban domin kowa zai goyi bayanmu ciki da wajen filin wasa, kuma muna son su goyi bayanmu har zuwa ƙarshe."

"Misali da muka fafata da Manchester City, magoya baya ne suka zaburar da mu kuma yanzu muna son sake maimaita hakan," in ji Hakimi.