Kasuwar musayar 'yan kwallo: Makomar Neymar, Amrabat, da Raya

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United na fatan sake hada dan wasa Benjamin Pavard, mai shekara 27, tare da tsohon abokin tamaular shi na Faransa kuma bayan Red Devils, Raphael Varane, mai shekara 30, kan farashin kusan fam miliyan 26, kamar yadda aka taya mai tsaron gidan Bayern Munich. (L'Equipe - in French)
Manchester United ma na son dauko dan wasan Moroko Sofyan Amrabat, mai shekara 26 kan farashin fam miliyan 30. (Mail)
Sai dai duk da hakan, Amrabat ya fi son komawa taka leda Atletico Madrid domin su hade da Diego Simeonea wannan kakar. (Sport - in Spanish)
Jami'an dan wasan gaba na Brazil, mai taka leda a Paris St-Germain wato Neymar, za su gana a wannan makon a kokarin tattauna makomar dan wasan mai shekara 31, ciki har da kawo karshen kwantiraginsa da kungiyar idan bukatar hakan ta taso. (UOL Sport Brasil - in Portuguese)
Chelsea na gab da kammala yarjejeniyar dauko dan wasan tsakiya na Ecuador, Moises Caicedo, mai shekara 21, daga Brighton, sun kuma kagu su kallama komai domin ya fara wasan farko a asabar din nan a karawar da za su yi da Liverpool. (Guardian)
Tsohon shugaban Blues Thomas Tuchel da ke jagorantar
Bayern Munich ya fara fakon mai tsaron ragar Sifaniya, da ke taka leda a Chelsea Kepa Arrizabalaga, mai shekara 28, domin kai shi Bundesliga da fatan zai maye gurbin dan wasan Jamus Manuel Neuer mai shekara 37 da ya ke jinya. (Fabrizio Romano)
Chelsea ta yanke shawarar watsi da tattaunawar musayar dan wasan gaba na Sabiya Dusan Vlahovic, mai shekara 23, da mai kai hari na Belgium Romelu Lukaku mai shekara 30. (Sky Sport Italia - via Football Italia)
Dan wasan Brentford kuma mai tsaron ragar Sifaniya David Raya, 27, ya shirya tsaf domin tafiya zaman aro a Arsenal, sannan ya na zabin amincewa da kowa kungiyar a kaka mai zuwa, maimakon gaggawar komawa kungiyar dindindin. (Athletic - subscription required)
Kungiyar Napoli ta Italiya na zawarcin dan wasan gaba na Paraguay, da ke taka leda a Brighton Julio Enciso mai shekara 19. (Telegraph)
Bournemouth na shirin shan gaban Leeds United, a kokarin daukar dan wasan baya na Ingila da ke taka leda a Norwich City Max Aarons, mai shekara 23. (Athletic - subscription required)











