Saudiyya za ta karbi bakuncin wasan karshen na Spanish Super Cup

Real Madrid ce ta lashe kofin a wasan karshe da ta buga da Bilbao

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Real Madrid ce ta lashe kofin a wasan karshe da ta buga da Bilbao
An wallafa

Saudiyya za ta dauki nauyin bakuncin wasannin Kofin Sifaniyawanda za a yi a watan Janairun 2023, kamar yadda hukumar kwallon kafa ta Sifaniyan ta sanar a ranar Alhamis.

Za a yi daya daga cikin wasannin kusa da na karshe tsakanin gwarzuwar gasar Real Madrid da Valencia a babban birin kasar Riyad, haka wasan Real Betis da Barcelona.

Za a yi wasan karshe a ranar 15 ga watan Janairu.

"Za a yi wasan nin a filin wasa na Sarki Fahad da ke Riyad mai daukar 'yn kallon 60,000" in ji hukumar.

Wannan ne karo na uku da Saudiyyar ke karbar bakuncin wasan kofin Sifaninsh, yayin da ake shirin yarjejeniyar daukar nauyin gasar a kasar har zuwa 2029.

A wasan karshe na 2022 Real Madrid ta doke Athletico Bilbao da ci 2-0.