An samu koma-baya a tsawon rai da ilimi a fadin duniya

Asalin hoton, Getty Images
An shafe shekaru da dama da samun ci gaba ta fuskar tsawon rai da ilimi da kuma ci gaban tattalin arziki a kasashen duniya.
To amma tun bayan zuwan annobar korona an samu koma baya a wadannan bangarori na rayuwa, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta sanar a rahotonta na ranar Alhamis.
Alkaluman da Majalisar ta fitar sun nuna cewa an samu koma baya ne a ma'aunin ci gaban dan adam a kasashe tara daga cikin 10 a shekaru biyu da suka wuce.
Kuma bala'o'i kamar na annobar korona da yakin da ake yi a Ukraine da kuma barnar da sauyin yanayi ke yi ne suka ta'zzara ci bayan kasashen duniya.
Switzerland ce ke kan gaba a jadawalin ci gaba ta fuskar tsawon rai da shekaru 84, da ci gaba ta fannin ilimi inda dalibi zai iya kaiwa shekara 16.5 a makaranta, da kuma albashi mai kyau, wanda tsaka-tsaki zai iya kaiwa dala 66,000.
Sudan ta Kudu ce a ƙsan teburin, inda tsawon rai ba ya wuce shekaru 55, sannan ba a wuce sama da shekara biyar na karatu a mafi yawan lokuta, kazalika albashi bai wuce dala 768 a shekara.
Koma bayan da aka samu a mafi yawan kasashe da yawansu ya kai 191 musamman ta fannin tsawon rai sun sa an koma inda aka fito, kamar a alkaluman da aka gani a 2016.

Alal misali a Amurka, tsawon rai daga haihuwa ya yi kasa da shekaru biyu tun 2019. A wasu kasashen koma bayan ya yi muni sosai.
An fara kididdige yadda ci gaban dan adam ke tafiya ta fannoni daban-daban a shekarar 1990, a wani yunkuri na sauya ci gaban al'umma ta wasu fuskoki baya ga karfin tattalin arzikin da kasashe ke da shi.
A tsawon shekaru kasashe da dama sun fuskanci tashe tashen hankula da ci baya, to amma alkaluman bara sun fi nuna ci bayan a zahiri.
Duk da haka kashi biyu bisa uku na kasashe masu arziki sun farfado, yayin da kasashe da dama ke ci gaba da fuskantar tabarbarewar al'amura.
Alkaluman bana na bayyana sakamakon da aka samu ne daga shekarar 2021, sun kuma nuna cewa sama da kasashe 80 na fuskantar matsalar gaza biyan bashin da ake bin su, a cewar Achim Steiner, daya daga cikin kwararrun da suka gudanar da aikin.
''Kasashe 80 na dab da fadawa cikin mummunan yanayi, don muna ganin yadda lamurra ke tabarbarewa kuma da yiwuwar a cigaba da ganin hakan a shekaru masu zuwa.''











