Yara masu larurar nakasa na fuskantar cin zarafi a Ukraine – MDD

..
An wallafa

Ƙwararru daga Majalisar Dinkin Duniya sun yi gargaɗin cewa ana cin zarafin ƙananan yara masu larurar naƙasa tare da watsi da su a cibiyoyi daban-daban a Ukraine.

Jami'an hukumar kare haƙƙin bil adama na Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce yaƙin da ake yi ya sa halin da waɗannan yaran ke ciki ya ƙara tsanani inda suka yi kira ga gwamnatin ƙasar ta yi gyara kan irin kura-kuran da take tafkawa.

Wannan rahoton nasu na zuwa ne bayan wani binciken BBC ya bankaɗo yadda ake cin zarafin yara a gidajen marayu a faɗin ƙasar.

Akwai sama da yara 100,000 da kuma matasa da ke zaune a irin waɗannan cibiyoyi kafin soma yaƙi a Ukraine.

A lokacin da Rasha ta yi kutse cikin Ukraine a watan Fabrairu, akwai dubban yaran da aka cire su daga waɗannan gidajen marayu aka mayar da su ga dangin su.

Ƙwararru a Majalisar Ɗinkin Duniyar sun koka kan cewa wannan matakin da aka ɗauka ya ja waɗannan yaran ba su da wani gata kuma hakan ya jefa su cikin barazanar cin zarafi da rayuwa kan tituna da kuma zama cikin waɗanda masu safarar bil adama ke hari.

Sai dai duk da haka akwai sauran wasu dubban da ke rayuwa a irin waɗannan cibiyoyi kusan 700 a faɗin Ukraine duk da cewa irin waɗannan cibiyoyi ana kiransu da gidajen marayu, amma kashi 90 cikin 100 na yaran da ke zaune a irin waɗannan gidaje na da iyaye ko dangi.

A zamanin da da kuma na yanzu duk an yi itifaƙi a Ukraine kan cewa yara masu fama da larurar naƙasa sun fi samun kulawa mai kyau a irin waɗannan cibiyoyi.

A watan Yunin da ya wuce, BBC ta kai ziyara gidajen marayu biyar a kudancin Ukraine inda aka ga yara ɗaure a jikin bencina wasu kuma ɗaure a gefen gado, da dama daga cikinsu na fama da yunwa.

..