Tuchel zai koma Chelsea ko Man Utd ko Barca, Arteta ya ce sai ya yi sauyi

Asalin hoton, PA Media
Thomas Tuchel na son sake komawa Chelsea idan ya bar Bayern Munich a bazara to amma kuma kociyan dan Jamus na son zuwa Manchester United da Barcelona. (Sky Sports Germany)
Masu Liverpool sun gana da Michael Edwards a ranar Lahadi domin shawo kan tsohon darektan wasanni na kungiyar domin ya saita kungiyar bayan da Jurgen Klopp ya tafi. (Guardian)
Kociyan Arsenal Mikel Arteta ya ce kwazon da kungiyar ke yi a yanzu ba zai sa ta sauya shirinta na saye da sayar da 'yanwasa ba, inda ake sa ran Gunners din za su sayi mai kai hari a bazara. (ESPN)
Newcastle United da Bayern Munich, na son dan bayan Arsenal Oleksandr Zinchenko, wanda Gunners din ke son fam miliyan 38.5 a kan dan Ukraine din.(Football Transfers)
Wakilindan wasan gaba na gefe na Georgia Khvicha Kvaratskhelia, ya ce matashin danwasan zai bar Napoli idan kungiyar ta Italiya ta samu tayi mai kyau a kansa. (Gazzetta dello Sport)
Ana sa ran shugabannin Manchester United su hana Mason Greenwood tafiya rangadin wasannin shirin tunkarar sabuwar kaka da za su tafi Amurka idan dan wasan na Ingila ya koma daga aron da ya tafi Getafe. (Star)
Greenwood na daya daga cikin 'yanwasan da watakila Barcelona za ta saya, kasancewar tuni an tattauna a kan cinikinsa a bazara. (Sport)
Chelsea za ta dogara ne a kan ribar da za ta samu a bazaran nan wajen sayen 'yanwasan da take so, inda za ta mayar da hankali wajen rage matasan 'yanwasan da ta rena irin su Conor Gallagher, da Trevoh Chalobah, da Armando Broja, na Albaniya mai shekara 22. (Teamtalk)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dan wasan gaba na gefe Chelsea ta fi son saye a yanzu inda take sa rai da samun matashin dan wasan Leeds United Crysencio Summerville, na Holland. (Teamtalk)
Masu Chelsea na fuskantar matsin lamba daga magoya bayan Strasbourg a kan su sauya tsarinsu na saye da sayar da 'yanwasa kasancewar ba su yi kokari ba a bana, tun bayan da BlueCo suka sayi mafi yawan hannun jarin kungiyar ta Faransa a watan Yuni da ya gata. (90min)
Manchester United sun tattauna domin tsawaita kwantiragin matashin dan wasansu na Ingila Kobbie Mainoo sakamakon yadda mai shekara 18 din ya taka rawar gani a bana. (Manchester Evening News)
Wasu kungiyoyin gasar Premier da na waje suna bin diddigin matashin danwasan Birmingham City Tobey Ugorji, mai shekara 16, wanda ya cancanci buga wa Ingila da Najeriya wasa. (Football Insider)
Everton na kan gaba wajen samun damar sayen matashin danwasan gaba na Ireland Mason Melia, mai shekara 16, daga Athletic ta St Patrick (Football Insider)










