An daɓa wa magoya bayan Brighton biyu wuƙa a Rome

Asalin hoton, Getty Images
An caka wa magoya bayan ƙungiyar Brighton & Hove Albion biyu wuka a birnin Rome kafin wasansu na gasar cin kofin Europa League da AS Roma.
Wasu gungun mutane bakwai ne suka afka wa mutanen biyu a daren alhamis amma sun yi nasarar samun tsira a wani shago bayan a ji musu raunuka a ƙafa.
Rahotanni sun bayyan cewa an kai mutanen asibitoci daban-daban domin samun kula.
Kimanin magoya bayan Brighton 3,500 ne suka je birnin Rome domin kallon wasan farko a zagaye na biyu da ƙungiyar za ta fafata.
Jami’in hulɗa da ƴan sandan Albion na rundunar ƴan sandan Sussex Darren Balkham ya ce ya yi magana da magoya bayan Albion ɗin biyu, kuma ya ce dukkansu suna cikin ƙoshin lafiya.
Babu wata alama da ke nuna ko maharan magoya bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta AS Roma ne.
An shawarci magoya bayan Brighton da ke halartar wasan da su yi amfani da ababen hawa na kyauta da aka tanadar domin zuwa filin wasan Stadio Olimpico.







