City za ta iya sake lashe Champions League - Guardiola

Asalin hoton, Getty Images
Kafin ta lashe gasar zakarun Turai a kakar wasan da ta wuce, Manchester City ta yi kasa a gwiwa a gasar na tsawon kaka shida a jere, inda ta kai wasan daf da na kusa da ƙarshe sau uku, sannan ta yi wasa sau ɗaya a zagayen ƴan 16, da na kusa da na ƙarshe sau ɗaya da kuma na wasan ƙarshe sau ɗaya.
Ta na neman kare kambinta a kakar wasa ta bana wanda aka shirya buga wasan ƙarshen gasar a filin wasan Wembley ranar 1 ga watan Yuni.
Bayan wasan daren jiya, Pep Guardiola ya amince cewa akwai rashin ƙwarin gwiwa a kulob ɗin game da lashe gasar zakarun Turai a lokacin da ya zo ƙungiyar, amma ya jinjina wa mamallakan City saboda goyon bayan da suka ba shi don samun nasara a kakar wasan 2022-23.
Ya ce: ''Kafin in iso ba mu yarda cewa za mu iya ba. Abu ne da ke buƙatar lokaci da tsari. Sun ba ni lokaci, sun ba mu lokaci''.
Guardiola ya ƙara da cewa, "Mu ƙungiya ce da ke da yaƙinin cewa za mu iya yin hakan, muna fafatawa da Real Madrid da Bayern Munich, ba mu san wanda za mu fuskanta ba, magana ce ta mu sa ido mu gani, muhimmin abu shi ne shekara bakwai a jere ke nan muna wannan matakin."







