Me ya sa PDP ta sake ɗage babban taronta?

Asalin hoton, PDP
Jam'iyyar PDP a Najeriya ta yi ƙarin haske dangane da dalilan da suka sa ta ɗage gudanar da taron ƙolin jam'iyyar da aka shirya gudanarwa a ranar 13 ga watan Maris din nan zuwa 15 ga watan Mayu.
Ta ce ta ɗage taron ne saboda rashin kamala zaɓen shugabancin jam'iyyar a wasu jihohi da ƙananan hukumomi da mazaɓu musaman a yankin kudu maso gabashin ƙasar.
Mataimakin sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar, Ibrahim Abdullahi ya shaidawa BBC cewa ya zama dole ayi waɗannan zaɓuka kuma sun zo dai dai da lokacin da jam'iyyar za ta gudanar da babban taronta a ranar 13 ga watan Maris.
'' Daya daga cikin zaɓuɓɓukan shi ne zaɓen yankin kudu maso gabas wanda shi ne kusan ya ke ci mu na tuwo a ƙwarya''
''Kusan ƴan uwansa da ya kamata ayi su tare, duk an riga an yi su, shi ya sa mu ka ce a ɗaga zuwa watan Mayu,'' in ji shi.
Tuni bayanai suka nuna cewar wasu ƴan jam'iyyar sun fara guna guni ta ƙarƙashin ƙasa, ganin yadda ake ta ɗage wannan taron da ake ganin zai iya zama matakin warware ɗimbin rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar.
Sai dai jam'iyyar ta ce wannan zama ba zai iya ɗinke dukkanin matsalolin jam'iyyar ba.
''Wannan zaure bai iya ɗinke duk matsalolin jamiyyar, shi yasa ake da kwamitin gudanarwa kuma mu na nan mu na abinda ya kamata mu yi, ko ɗaga wannan taron zuwa 13 wanda shi ne aka sake ɗagawa yanzu da yawun zauren gwamnoni ne wanda aka yi a jihar Delta''
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Jam'iyyar ta kuma musanta zargin da wasu ke yi akan cewa shugabanta na riƙo Ambasada Umar Damagum na amfani da ɗagewar ne don tsawaita wa'adin mulkinsa
''Kundin tsarin mulki ya riga ya tanadar masa da wa'adin da zai yi a kan kujera na ba bu iyaka, da aka riga aka yanke na idan ya karɓi riƙon ƙwarya, wanda shi ne zai kai mu har zuwa watan Disamba na shekarar nan'', in ji shi
Sai dai tuni wasu masana suka fara tsokaci kan tasirin ɗagewar wajen ɗinke ɓarakar da jam'iyyar ke fama da ita.
Farfesa Abubakar Kari malamin kimiyar siyasa a jami'ar Abuja ya ce ɗage taron bai ba da mamaki ba:
''Har yanzu manyan muƙarraban wannan jam'iyyar adawa ta PDP ba su sami bakin zaren ba ne, ina ga suna jin tsoron kada a je taro, taron ya batse, ba a cimma wani abin a zo a gani ba''
'' Ci gaba da rashin sasanta wannan rikici da kuma sanin makomar jam'iyya saboda shi wannan taro babban abinda ake tsamani zai cimma shi ne a samu matsaya game da shugabancinta'', in ji shi.
A yanzu dai jam'iyyar ta mayar da ranar babban taronta zuwa 15 ga watan Mayun 2025.
Tun a bara ne aka saka ranar babban taron na 98 amma ana ta ɗagewa, wanda wannan ne yasa wasu ke ganin hakan bai rasa nasaba da wasu matsaloli na cikin gida da jam'iyyar ke fuskanta ba.














