'An bai wa mayaƙan ƙasashen ƙetare muƙamai a rundunar sojin Syria'

    • Marubuci, Sebastian Usher
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Damascus
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 3

Rahotanni sun bayyana cewa shugabannin Syria sun bai wa wasu masu ikirarin jihadi daga wasu ƙasashe manyan muƙamai a rundunar sojin ƙasar.

Ƙungiyar Hayat Tahrir al-Sham (HTS), wadda ta karɓe iko da ƙasar ce ke sake fasalin rundunar sojin ƙasar – tun bayan tuntsurar da gwamnatin tsohon shugaban ƙasar, Bashar al-Assad.

Duk da cewa shugabannin ƙungiyar ba su tabbatar da faruwar hakan ba, ana ganin lamarin zai haifar da damuwa kan rawar da ake tunanin masu tsattsauran ra'ayi za su taka a tafiyar da lamurran ƙasar.

Majiyoyi da dama a Syria sun tabbatar da cewa daga cikin sabbin muƙamai kimanin 50 a rundunar sojin ƙasar da aka sanar, shida daga cikinsu an bai wa wasu ne daga ƙetare.

Sunayen da aka wallafa na waɗanda za a bai wa muƙaman ya nuna cewa a ciki har da ƴan ƙabilar Uyhur na China, da wasu ƴan asalin ƙasashen Jordan da Turkiyya.

Dukkaninsu sun samu manyan muƙamai da suka kama daga kanar zuwa birgediya-janar.

Akwai dai sa hannun mayaƙa daga ƙasashe da dama a tashin hankalin da ƙasar ta Syria ta yi fama da shi.

Dubban mayaƙa daga ƙasashe da dama ne suka shiga cikin ƙungiyoyi masu yaƙi da Bashar al-Assad a lokacin da lamarin ya rincaɓe bayan matakin da jami'an tsaro suka ɗauka na murƙushe masu zanga-zanga da ƙarf.

Wasu sun kafa nasu ƙungiyoyin, yayin da wasu kuma suka shiga ƙungiyar IS, wadda ta karɓe iko da yanki mai yawa na gabashin ƙasar ta Syria.

A tsawon lokaci, masu adawa da ƙungiyat HTS sun zarge ta da kasancewa ƙungiyar da ke da mayaƙa daga ƙetare masu yawa – wani dalili da magoya bayan Assad suka yi amfani da shi domin sukar ƙungiyar yayin da ta yunƙuro domin kawar da tsohon shugaban.

Tun bayan karɓe iko da Syria, Ahmed al-Sharaa ya sha nanata cewa babbar manufarsa ita ce haɗe kan ɗaukacin Syria, ta yadda kowa zai ji ana yi da shi.

Ana ganin cewa ya bai wa mayaƙan ƙasashen waje muƙaman ne domin saka musu – saboda rawar da suka taka a nasarar da ƙungiyar HTS ta samu.

Kuma ana ganin cewa a kan wannan dalili, zai iya yiwuwa wasu daga cikin irin waɗannan mayaƙan na ƙetare su samu takardar zama ƴan ƙasar Syria.

Sai dai hakan zai iya zama ɗaya daga cikin abubuwa masu sarƙaƙiya da za su kawo cikas ga sabuwar Syria da ake kafawa.