Syria ba barazana ce ga duniya ba - Ahmed al-Sharaa

    • Marubuci, Jeremy Bowen
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, International Editor, BBC News
    • Aiko rahoto daga, Damascus
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 2

Shugaban Syria na wucingadi, Ahmed al-Sharaa ya ce ƙasar ta gajiya saboda yaƙe-yaƙen da ta yi fama da su saboda haka ba barazana ba ce ga maƙwabtanta ko ƙasashen yammaci.

A wata hira da BBC a birnin Damascus, al-Sharaa ya nei da a ɗage wa Syria takunkuman da aka aza mata.

"Yanzu, bayan duk abubuwan da suka faru, dole ne a cire wa Syria takunkumai saboda an aza su ne a kan tsohuwar gwamnati ne. Bai kamata a yi mu'amala iri ɗaya da macuci da wanda aka cuta ba.," al-Sharaa ya ce.

Sharaa ne dai ya jagoranci boren da ya tunɓuke mulkin Bashar al-Assad ƙasa da makonni biyu da suka gabata.

Shi ne shugaban ƙungiyar Hayat Tahrir al-Sham (HTS), ƙungiyar mafi ƙarfi a cikin haɗakar ƙungiyoyin tawaye, sannan an fi sanin sa a baya da inkiyarsa ta Abu Mohammed al-Jolani.

Ya ce ya kamata a cire ƙungiyar HTS daga jerin ƙungiyoyin ta'addanci. Ƙasashen Amurka da Burtaniya da Tarayyar Turai da Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran ƙungiyoyi da dama dai sun ayyana ƙungiyar a matsayin ta ta'addanci, kasancewar ta ɓalle ne daga ƙungiyar al-Qaeda a 2016.

Sharaa ya ce HTS ba ƙungiyar ta'adanci ba ce.

Ba sa kai hare-hare kan fararen hula ko wuraren jama'a, in ji shi. Suna ma kallon kansu a matsayin waɗanda gwamnatin Assad ta zalunta ne.

Ya kuma ƙi amincewa yana son ya mayar da Syria kwatankwacin Afghanistan.

Sharaa ya ce ƙasashen biyu suna da banbanci na al'ada. Afghanistan ƙasa ce mai ƙabilanci. A Syria kuwa ya ce na da mutane masu ra'ayi daban.

Ya ce ya yi imani da ilimin ƴaƴa mata.

"Muna da jami'o'i a Idlib yau fiye da shekaru takwas," Sharaa ya ce, wato yana nufin lardin arewa maso yammaci da ya zamo a hannun ƴantawaye tun 2011.

"Ina tunanin yawan matan da ke jami'ar ya fi kaso 60."

Da kuma aka tambaye shi ko za a ƙyale a sha giya, Sharaa ya ce: "Akwai abubuwa da yawa da ba ni da damar da zan yi magana a kansu saboda batutuwa ne da suka shafi shari'a."

Ya ƙara da cewa za a samu "kwamitin masana shari'a na Syria da za su rubuta kundin tsarin mulki. Za su samar da matsaya. Kuma dole ne kowane shugaba ya bi dokokin."

Hankalin Sharaa ya kasance a kwance a lokacin tattaunawar gabaɗaya, inda yake sanye da kayan gida yana mai ƙoƙarin shaida wa waɗanda suke tunanin ƙungiyarsa ba ta raba gari da ƙungiyar ta'addanci ba.

Ƴan Syria da dama dai ba su yarda shi ba. Yanzu abin jira a gani shi ne ayyukan da shi shugaban na Syria na wucingadi zai aikata a watanni masu zuwa domin gane irin alƙiblar da suke so Syria ta zama - da kuma yadda suke son jagorantar ta.